Facebook SDK


 AKAN AIKIN MIJINA!🧟👹🧟* _FREE BOOK_




        



      *AKAN AIKIN MIJINA! 🧟👹🧟* _FREE BOOK_




 _Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_               

          


   

     _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._


   ```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA...Free book... (32) ƘARAR KWANA PAID BOOK ₦300..(33) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (34) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (35) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (36) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is 

loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```


          _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *AKAN AIKIN MIJINA! 🧟👹🧟FREE BOOK*                             


      _Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._


*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*


................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓


........................


_BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM_





  *Page 1 to 5*




       ........Zaune take Cikin Wani k'asaitaccen parlour ya k'ayatu Sosai Domin kallo d'aya zaka masa kasan Ankashe naira gurin babu Abunda babu Aciki, itakanta idan ka kalleta zakasan hutu k'ud'i naira suna Aiki gajikinta saidai idan kayi mata kallo da idanuwan basira zaka fahimce dakwai damuwa tareda ita, kyakykyawace iya gwargwado Domin bazaka kirata Mummuna ba saidai batada fari sosai Kuma bazaka kirata bak'aba samu iya kiranta chocolate color Musamman da yanayin Hutu da k'ud'i suka zauna cikinta sai kyawonta yak'ara bayyana, bakinta k'arami lip's d'inta maishawar kalla tanada idanuwa madaidaita tanada gashi duk da bamai tsawo bane Sosai, itad'in dai Masha Allah, saidai gadukan Alamu dakwai damuwa tareda zuciyarta Domin kuwa yanzu Hakan zaune take Saman 2 seater tana sanye dawasu ringada wando pink color da hularsu masu taushi, tazabga Uban tagumi, can tanisa Tareda kai dubanta Zuwaga Agogon d'akin k'arfe 12:30 pm Amma duk wannan tsohon daren wai maigidan bayanan tarasa wane Irin Mahimmanci Aikin mijinta yakeda Wanda harbayaji baya Gani gansa Kuma baida lokacin iyalansa Yazab'e Aikinsa sama da Farincikinta, tana zaune ne cikin damuwa da kad'aici gamida K'unci duka Badan komai ba Saidan kawai *AKAN AIKIN MIJINA* Zuciyar tafara mata Wani zogi take Kanta yasoma sarawa ganin tana neman illatakanta *AKAN AIKIN MIJINTA* yasa tamik'e tanashare wasu hawaye masu zafi dakeson zubomata TV Dake d'akin yanata Aiki shi K'ad'ai Domin ko kad'an hankalinta baya garesa yasa tamik'e takasheshi Tareda kashe wutar d'akin tarufe k'ofar parlour tanufe bedroom d'inta saidai me,? Harta shiga d'akin taji TV yana magana kuma Tareda bayyanar haske kuma bayan tasan takashe, tsayawa tayi cak Tareda juyowa baya ganin lalle TV D'in kunne yake Kuma gasken d'akin Shima, A fili tace"A'a dama wai ban kashe TV bane? Kodai damuwar *AIKIN MIJINA* tana neman haukatar danine,"? Batada Wanda zai bata Ansa Hakan yasa tasake komawa tasake kashe komai tasake juya tana k'ok'arin rufe k'ofar bedroom d'inta tasake jin K'aran TV wannan karon tad'an tsorota Domin tasancewar tabbas takashe TV dube dube tafara Amma bakowa Kuma ba komai cikin k'arfin hali da tsoro Takoma saita cire socket D'in duka tasake kashe wutar d'akin Cikin sauri tashiga bedroom D'in saidai tinkan takaiga rufewa tasake jin K'aran TV Cikin tsoro tasake waigowa idanta yakai kan socket D'in saidai Abun mamaki ganin socket D'in k'asa baya ciki tasake Kai idanta kan TV Kuma yana Aiki, jabaya tafara cikin tsoro gamida firgici bata k'ara tsinkewa ba saidai taga wuyar d'akin tasoma kunnawa da kashewa dakanta cikin TV kuwa wasu Mutane fuskarsu rufe da janyadi suka soma zagayar Wani Dake tsakansu shiba zaune ba shiba tsaye ba saidai yanada GIRMAN gaske Kuma duka jikinsa na hayak'ine kamar hayak'in wuta Hakan yake Amma Kuma ko wacce siffa yanada saidai babu k'afar takawa Irin ta Mutane wata kan k'aface Daban Wadda zata tabbatar Maka cewar shid'in ba mutum bane Aljanine, jabaya tafara Domin kuwa duka sunmaida halinsu gareta dukda su fuskarsu rufe take, hannayensu suka soma d'agawa tareda nufo inda inda take Kuma suka soma fitowa daga cikin TV D'in saidai har lokacin shi yana Zaune Bai motsa ba Kuma Bai waigowa yakalle taba, jabaya take Cikin tsananin tsoro gamida fargaba cikin sauri tasoma k'ok'arin rufe k'ofar Amma Abun mamaki kawai saitaganshi shi Wannan Mai siffar hayak'in gabanta , Wani Uban ihu tarabka Wanda duka gidan Saida ya Ansa take Kuma tafad'i k'asa gurin.................

.......



Page 6 to 15*




           "Subhanallahi baba Audu kaji ihun hajiya kuwa,"




   "Nima wallahi ihundanaji ne yafito dani danni harna fara gyangyad'i,"




"Kodai mushiga muduba meke faruwa,"? 



  

 "Habadai sale taya zaka shiga gidan Mutum bayanan har ciki inda iyalinsa,"? 




 "To Amma ai kamawa tayi baba Audu Kuma idan zaka lura ai Koda Dr yananan nakan shiga parlour tinda Nike karb'ar guga ko sayen wasu Kayan cefane"





  "Eh nasani duk da Hakan dai gara kafara Kiran shi Dr D'in Kaga yasan halinda Ake ciki"




  Wayarsa Sale yaciro A Aljihunsa yasoma Kiran Dr saidai harta gama ringing Bai d'auka ba,



"Bai d'auka bane sale"




"Eh wllh Baid'auka ba Amma bari nasake gwadawa nagani"




Sake Saka Kiran yayi kusan 3 messed call yamasa Ana 4 yaji wayar switch off


Sake Baki yayi yana kallon wayar




"Yaya dai Bai d'auka D'in ba? Koyana cikin Aikine kasan fa su likitawa Musamman idan sunada girma da k'warewa basucika samun Hutu ba,"





 "Haba Dan Allah baba Audu Aikoda Aiki wllh da mugun hali fisabilillahi kakira Mutum Irin wannan lokacin Kuma bayan yasan baka saba kiransa ba kakira yanzu Dan walak'anci tayi ringing harta gama yak'i d'auka daga k'arshe waisaiya kashe wayarsa Kai wannan bawan Allah Rayuwarsa da gyara wallahi Hajiya tana k'ok'arin zama dashi,"





  "Sale kasanfa yanayin Aikinsa Kuma idan yana cikin Wani Uzurin nefa,"




"Dan Allah kadaina ganin kamar baida laifi wallahi ni indai gameda Aikinsa ne har Haushinsa nakeji Domin baida lokacin kowa da komai saidai Aikinsa shidai Aiki Aiki saikace garesa Akafara Aikin likitancin Ace *AKAN AIKIN MIJINA* baida lokacina habadai baba Audu kaduba wllh konida bawani nake cikin gidan ba nasan Hajiya tana cutuwa Badan komai ba Saidan *AKAN AIKIN MIJINTA* ni wllh dazan ga Y'an Uwanta nasamu damar magana dasu wllh saina fad'a musu halinda take ciki Wllh "






Sake Baki baba Audu yayi cikeda mamaki yace"Sale, Sale baruwanka shifa Baki shike Yankee wuya babu ruwanka kada kasake kayi wannan gangancin wllh babu ruwanka, Kuma yanzu darene gashi batasake ihun ba saboda haka kaje kakwanta yafi nima zankwanta Allah yakawo muna sauk'i"




Yana k'ananan gunguninsa yawuce ciki suma suka kwanta...




Washe gari sai kusan k'arfe 9:00 Am nasafe yadawo gidan hong yadanna Baba Audu yabud'e Masa, direct inda Akatanada Domin Aje motoci yashigarda tasa, fitowa yayi Ahankali hannunsa narik'e da jakarsa da lapcort D'insa sai wayoyinsa kallo d'aya zaka masa kahango gajiya taredashi, inda babu Audu ya tsaya suka gaisa cikin mutunci da girmamawa yanufi ciki gaskiya shi D'in maikyau ne Domin shiba dogo sosai ba Kuma ba gajere ba saidai yanada haske Sosai kamar idan katab'a shi jini yafito Musamman yanayin kalan Hutun da yake samu kansa d'auke yake da lallausan suma haka fuskarsa ta k'awatu da sake zuwa gemunsa Kai kawai ku hasko kyawonsa da kanku reader nabaku damar Amma doctor Muhayseem kam maikyau ne Ajin farko Acikin maza ga k'ud'i Kuma ga ilimi gamida Hutu, k'wararren likita ne kan Abunda yashafe fid'a indai shiga theater ne takan ko wane b'angare to doctor Muhayseem yayi fice Anan Domin har K'asan waje yake fita gudanarda Aikinsa, bayan gama master's d'insa can k'asar Indonesia sunso yasoma Aiki dasu Amma iyayensa suka hana kan saidai yataimake k'asarsa Nigeria Shima yanada ra'ayin hakan yasa yadawo gida Nigeria cikin iKon Allah Allah ya had'asashi da Muhseena Wanda kallo d'aya Yamata Allah yajarabceshinda mugun sonta cikin Amincewar Allah Akayi bikinsu,.



Parlour rufe yayi Mamakin ganin har k'arfe 9:00 nasafe parlour rufe master key d'insa ya d'auka yabud'e yashiga parlour da kallo yabi parlour Shima tsit babu kowa Kuma babu motsinta Anan, baikawo komai Aransa ba direct yawuce d'akinsa yarage Kayan jikinsa yashiga wanka, Koda yafito idanuwansa har rufewa suke saboda bacci Hakan yasa yazura jallabiyansa kawai yahaye gadon Tareda k'ara gudun AC yasoma bacci...........




PAGE 16 TO 20*



    .........Sallama taketa faman Shirgawa Amma Shuru hakan yasa tanufe bedroom D'in nata tareda nocking nanma Shuru natsuwa tayi tafeda kara kunnenta jikin k'ofar waikotaji motsinsu amma shuru Hakan yasa tatura k'ofar kaitsaye tashiga da sallama tanad'an d'ari d'arin shiga Domin taga motor Yayanta waje tasan ko yanagidan, bakowa Hakan yasa tak'arasa shiga ciki jin tad'an Shure Wani Abu yasa cikin sauri tsaya Tareda Maida Kanta k'asa, ganinta kwance K'asan yashe kamar ma bata numfashi yasata tsorota tad'an jaba kad'an kafin Kuma tasunkuya gareta tana tab'a jikinta Tareda fad'in "Aunty Muhseenarh meke faruwa Dake kina kina kuwa,"?


Ganin Shuru bata motsaba yasa tamik'e da sauri tad'ako ruwa masu sanyi tashafa mata A fuska Tareda yayyafa mata Ajiki, dogon numfashi taja kafin tasoma k'ok'arin Bud'e idanuwanta Tareda sakin k'ara saurin rik'eta Haimat tayi tana fad'in "Subhanallah Aunty waimeke faruwane nice Haimat fa, kinatsu Aunty,"


Ahankali tashiga Bud'e idanuwanta dasuka Mata nauyi Kanta tamkar yatsage saboda ciwo, dataimakon Haimat tasamu tamik'e gefen gado tazaunar da ita tanamata sannu, d'an dafe Kanta tayi nad'an lokaci batareda ta Ansamata ba ita kad'ai tasan yarda takeji gameda ciwon kanta,




"Aunty dama bakida lafiya? Wai Ina yayane har kikashiga Irin wannan halin?, Amma bayana gidan ba bari nakirashi,"




Sai Alokacin cikin k'arfin hali tad'ago tana yamutsa fuska tace"A'a barshi Kinga yana gurin Aikinsa kada mud'agamasa Hankali yakasa yin Abunda yajeyi zansamu relief ai bari nasha maganin saina kwanta kafin Ajima kad'an zandawo daidai,"




   "Amma Aunty meye Amfanin Aikinsa da k'warewarsa bayan Agida matarsa tana buk'atar kulawa Amma yaje waje yana badawa, waima yaya Akayi kika fad'i Anan,"?




Jintanbayar Saida gabanta yafad'i Domin tunowa da Abunda yafaru to kodai tafad'a matane? Amma idan tafad'a mata saita tanbayeta Ina Muhayseem yake? Batason kuwa yasan halinda take ciki balantana yaji Wani iri kan mijinta, Kuma batason duniya tasancewar *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Farinciki har nasoma Arba da Aljanu, 




"Aunty Anya kuwa babu matsala naga kin fad'a dogon tunani wai meke faruwa ne Anya kuwa ya Muhayseem bada Saka Hannu Cikin shigarki wannan Halin,"?




 

 "A'ah A'ah Haimat kadama kikawo wannan tunanin lafiya qlu muke kawai tsantsine ya kwasheni bayan nafito daga gurin Alwala to saina suma shine kawai Amma bakomai Kuma nahana kigayamasa ne saboda kada A d'aga masa Hankali Amma bakomai,"





"Shikenan Auntie Allah yatsare Gaba dama nazo gurin Aunty Jamila ne shine nabiyo tanan tace Agaidaki Kuma ga Sak'o tace Abaki zakuyi waya inaganin sak'on daga Auntie kubra ne Domin Saida nabiya Tasha na Anso nakaimata tace nakawo nakine zakuyi waya"




Cikin yak'e tace Allah sarki nagode ai kam Auntie kubra Yanzu tadaina son Zaman Nigeria gaba d'aya" 

Tak'arasa maganar tana mik'ewa




"Ai wllh Auntie tahuta Nigeria kam ai sai Ahankali nikaina da hajiya zata barni kodayake ba hajiya ce Mai matsalar ba kamar wannan Mijin naki Yaya Muhayseem yanada matsala Yanzu zaice fita waje ga macce badaidai bane Abari saitayi Aure"





"To tanan Zaki b'ullo togashinan yana jinki"

Tafad'a tana murmushi




Mik'ewa tayi dasauri tana dariya Tareda cewa"sai Anjima ninamar gidan Allah yak'ara lafiya" 




Wanka tasakeyi Amma Zuciyarta cunkushe take gamida tsoro, fitowa tayi tasaka Wani material tayi kyau saidai harta fad'a tayi rama kad'an sallan da batasamu tayi ba tayi, Ahankali tafito parlour tanad'an lek'awa Domin motsi taji shitagani Zaune yana tab'a laptop d'insa sai K'aramin Kofi Dake d'auke da lemu gabansa yana kurb'a hankalinsa kwance, 


Wani Irin takaici da b'acin rai taji yataso mata tindaga Zuciyarta zuwa bakinta, watoma yadawo D'in shine koya dubata yaje yacigaba da Aikin gabansa Kuma dan walak'anci Yanzunma Aiki toda Ace Haimat Bata biyowa tabata taimako Kenan Nan zata k'are inma mutuwace tamutu Yanzu ko Ajikinsa saboda yana *AKAN AIKINSA*, wasu hawaye masu zafi suka soma silalowa daga idanuwanta Kenan wannan Shine K'addaranta narasa kulawa Farinciki lokaci Badan komai ba saidan *AKAN AIKIN MIJINA* kowama d'akin tayi dasauri saboda Wani kuka dayazomata fad'awa tayi kan gadon tasaki kuka Mai narka Zuciyar maikaratu,



Jin kamar motsi yasa yad'aga kansa komawarta kawai yagani kamar Kuma kuka take, d'an dafe kansa yayi Tareda sakin salati yamik'e yashiga d'akin,


Kwance yasameta tayi ruf daciki tana kuka sosai maiban tausayi da sauri yak'ara kan gadon gamida janyota cikinsa cikin damuwa yace"Subhanallahi meke faruwane," 


K'wace jikinta tayi tasake komawa takwanta tacigaba da kukanta 



"Oh God my Lovely wife what Strong with you meke faruwane kimin magana kada ki d'agamun hankalina kinsan banason ganinki cikin Damuwa Dan Allah ki fad'amun make faruwane,"?



Yasake janyota jikinsa gaba d'aya sai Alokacin ta d'ago fuskarta takalleshi 


Ganin Yarda idanuwanta suka kumbura fuskarta tasoma ja saboda kuka Kuma gajijiyoyin kanta sun bayyana yasashi Cikin damuwa tareda tashin hankali Yace" Meya sameki duba kiga Nan harda tabo kamar kinbugu da Wani Abu, kanki yana ciwo ba ga Alamun gajiya taredake wai duka saboda me Hayateey" duk lokaci d'aya yake jefamata tanbayoyin cikin rud'u da damuwa Domin Allah yasani yana tsananin son Muhseenarh




Sake fisge jikinta tayi daga nasa Tareda watsa masa kallon rainin hankali tace"Har kanada bakinda zaka tanbayeni make damuwata? Aikasani *AIKIN KANE* babban damuwata komai Dake faruwa baduka *AKAN AIKINKA BANE* bakadamu da komai ba sai Aikin ka, 

Ina cikin damuwa ne badan komai ba face kawai *AKAN AIKIN MIJINA*.............



Page 21 to 30*




  ......."Yi hak'uri nasani bana kyautawa Kuma nasani nashiga hakkenki Amma ai kinsan inasonki ko,"?





 "Wannan shine Son Dr? Meye Amfanin sonda kake fad'a bayan bashi Azahiri, kawai dai Yanzu kadaina Sona tinda ka mallakeni kadaina kulawa Dani Yanzu dai babu wata soyayya data rake a Zuciyarka indai kaina ne," 





"Waya fad'a Miki? Ai soyayyar gaskiya bata sauyawa wife kiyarda Dani wifey wllh Ina Miki sonda bazai lissafuba know yarda dani indai kan wannan halinne zangyara Dan Allah kidaina shiga Irin wannan damuwar banaso, kilama ko Abinci bakici ba ko,"? Ya fad'a yanakai hannunsa kan Cikinta Rintse idanuwanta kawai tayi Tareda komawa ta kwanta dan haryanzu Kanta baidana Sara mataba,


Ganin tayi kwance Tareda rufe idanuwanta batace komai ba yasa yamik'e da Kansa Domin daiyagane fushi take dashi,



Komawa d'akinsa yayi yacire jallabiyan yasaka tree quieter yashiga kitchen D'in Kasancewar zaman hotels dayayi yasa yad'an iya dafa wasu k'ananan Abubuwa kamar Taliya ko indomie yanzunma Taliyan yadafa Mata Tareda kifi Saidai duk ya hargitsa kitchen D'in shikanshi yayi Wani wujga wujga dashi yagama dafawar yakashe electric D'in yazuba kan plate ya d'auko yanufi d'akin tananan kwance yabarta, K'aramin table D'in Glass Dake d'akin yajanyo ya d'aura plate D'in yakoma ya d'auko lemo ruwa Tareda spoon ya Aje yana sauke numfashi yace"Wifey zokici Abuncin nagama,"



Banza tamasa Hakan yasa ya k'arabo Tareda Kai mata kiss Agoshi yace"Haba my Love, my happiness Matar Dr Muhayseem kiyi hak'uri kitashi kici girkin Dr nasha wuya fa," yak'ara maganar yana sake sakin nishi,



Bud'e idanuwanta tayi Ahankali takalleshi ganin Yarda yake had'a Gumi duk jikinsa yab'aci harda kufan timatir A fuskarsa



Dariya tasaki Ahankali tamik'e Zaune tana kallonsa tana Cigaba da dariyar


D'an b'ata fuska yayi yace"Meye Abun dariya Kuma,"?




 "Dubeka saikace Wanda yayi Wani baban Aikin Taliya kawaii fa Kadafa Amma dubeka yarda kakoma" tak'arasa tana murmushi gamida matso da table D'in tana k'ok'arin cin Abincin




Gurin dressing mirror d'inta yanufa yakalle kansa murmushi yasaki yace"Wai haka nadawo Ashe harda Wani Duhu nayifa, Ai dole nakawo y'ar Aiki gidannan Dan Wllh mata Kuna k'ok'ari Aikin girki Akwai wuya wllh"





Hunmm"dama sai yanzu kasani, Ai shiyasa Ayuka dayawa Annabi Muhammad S.A.W yana taya Iyalinsa Ayuka Amma ku mazan Yanzu Allah dai ya kyauta ganin kuke kamar Raini ko kunci bayane saikuk'iy Aiko da koyawar Manzo dai tagurin tausayin iyaline wllh bakwayi guri d'aya kuke competition k'arin Aure, Koda yake Wani mijin ma *AKAN AIKINSA* baimada lokacin matarsa," tak'arasa maganar tanakai Abincin bakinta



Murmushi kawai yayi baiyi magana ba Domin yasan sarai dashi take, Kuma sanin baida gaskiya shiyasa Bai tankata ba,




Itakuwa tanasane tak'ara da fad'ar rashin lokacin, d'an b'ata fuska tayi tace"Amma fa girkin yayi gishiri K'ad'an waima kacishi Kuwa,"





"Inafa aike kawai nayiwa yanzu dai Dan Allah kiyi hak'uri komai yawuce kisamu kici kishiga magani Koda ciwon kan naki sai sauka, Maganar Mai Aikin zanyiwa Hajiya magana tasamamana Koda Uwanice saita bamu tadinga ragemiki wasu Aikin Amma kinsan banason girkinsu ko,"





 "Nikaina banaso gaskiya nidai kabarma y'ar Aikin kawai banaso,"



B'anlo mata maganin yayi yana bata yace"saboda me bayan rage miki Wahalan zatayi Kuma taragemiki kewanzama kafin nadawo"





Karb'ar maganin tayi tasha Tareda yamutsa fuska tace"Eh kam ai dole kasamun maitayin zama tinda Kai gidan yazama kamar kurkuku gareka, nidai banson Mai Aikin dan banson Abunda zaije yadawo gaskiya dama tsohuwace da sauk'i"




 "Bahaka bane dear wllh nikaina zaman hospital D'in bawai inasonshi bane A'a tawa K'addarance Hakan Kuma Kinga inataimakon rayuka ai Abun Alfaharine gareki my dear Ace mijinki yana taimakon Rayuwa, Hah to meyasa bakison yarinya sai tsohuwa? Bayan intsohuwa ce kezata d'aurawa Wani Aikin ma,"





 "Allah dai ya kyauta Amma Dai kadinga gyarawa gaskiya Abun yayi Yawa, oh yarinya kakeso saboda kasamu kayi ta biyun ko? Duk dama yanzu bansan me Ake k'ullawa cikin Asibitin ba Musamman yarda kake dagewa Kuma ai duk Wanda yasan masu Aikin lafiya da lecture's Malaman boko yasan su son mata Ajininsu yake,"





"Oh God yaude na lura masifa da neman rigima kikeji, Kinga tinda kinsha magani kikwanta kid'an huta idan kika tashi muje shan ice cream kozaki huce," yak'arasa maganar yana kashe mata ido d'aya tareda barin d'akin




Wani malalacin murmushi kawai tasaki tareda cigaba dacin Abuncinta Saida tagama tamik'e tamaida plate D'in nantaga Aikinda yajamata A kitchen D'in dole tahau gyarawa, 



Ruwa yawatsa yasake Saka wani trouser yafito Dama indai yana gida Bai iya zama da kaya Akwaishi da Jin zafi Shiyasa kullum cikin Ac yake, d'akin yakoma Baigantaba motsi yaji A kitchen yanufe can tsaye yaganta tana Aiki, shiga yayi yace"nasaki wahala ko Qalby,"?


Yak'arasa maganar yana rungumarta tabayanta Tareda d'aura kansa gefen kafad'arta yace"I miss you So much honey,"



Soma fitarda ita daga yanayinta yayi lura tasoma Ansar sak'onsa yasa yad'agata cak subar kitchen D'in,


Nidai gidan nabari gaba d'aya .........





"Amma ai ni likita ne ko inada damar ma'amala da mata dayawa tinda yanayin Aikine dole Kuma na sauraresu Tareda Basu kulawa saboda likita ne,"





 


"Ai dama tanan kukafi k'arfi da Anyi magana kuce Aiki Aiki shikenan Dan kana likita saikayita ma'amala da Mata wllh duka hakanan kuka dama Indai namiji yana Aikin Asibiti to wllh mafi yawancinku mabiya mata ne"





"Yasmin Nike fad'awa Irin wannan maganar,"?




"K'arya namaka ko bansan halinka bane? Wllh indai namiji Mai Aikin gafe Lafiya ne to bakuda Wani kamun Kai cikinku da wahala Asamu Wanda baibin mata,"





 "Yanzu kenan zargina kike daneman mata waje ,"?





"Ahaf kodai baka Aikata zinaba wllh kana mu'amalantar mata tinda kunsama kanku wannan muguwar tabi'a ko kunya bakuji sai kuyita sakin zance da Anyi magana kuce Aikinku dole ku Mu'amalancesu, kuyi Abunda yadace mana Wllh kuji tsoron Allah Domin A sanadin wannan Aikin inbaikaiku Aljanna ba wllh zai kaiku wuta,"




 "Yasmin, fatan shiga wuta kikemin *AKAN AIKINA* yaushe kika koma hakan waya sauya Miki ra'ayi yacusa Miki wannan Ak'idar,"?




"Au saiwani yacusamin? Hunm Abunda nasani nefa falsal kana Aikin Asibiti kace baka ma'amala da Mata? Hahaha Lalle nidai nafi k'arfin karaina min Hankalina Wllh Kuma nidai ni Yasmin Wllh bazaka sakamun Hawan jini ba, bazan kashe kaina Abanza ba *AKAN AIKIN MIJINA* kaje duk Wanda yagyara kansa Amma dai kaji tsoron Allah" mik'ewa tayi tabar parlour ranta fess koba komai ta rage zafinda yasa mata,



Shikuwa zama tareda dafe kansa yasoma tunanin waike shirin tuna Asirin *AIKINSA* ga Matar sa,"?........................


31 to 40*




  Zaune suke Parlour sai fira suke cikin Raha da nishad'i kwana biyun Nan kulawa tamusamman takesamu garesa Hakan yasa tak'ara kyau da jiki, Ayanzu Koda yaje Aikin baya Kai dare idan ko yakai tosuna lak'e da waya Kuma safiya nawayewazai dawo, Akwana biyun Nan Kuma tadaina ganin komai tadaina tsorata saboda yana gida suna tare,



"Kinshirya fito muje ko"




"Okay ganinan"


Fitowa tayi Cikin Shirinta rigada Zane na Atamfa tayafa mayafi babba tayi kyau sosai, kitchen Takoma tad'auko basket cikeda kuloli tafito


Lokacin yana danna wayarsa yabita da kallo yace"Ah inakuma Zaki da kayan Abinci haka saikace wadda zatayi tafiya,"?




"Hajiya nayiwa mana"




Karb'ar Kayan yayi yana fad'in "Zuwa inda hajiya kawai saikishiga lalura haka waima yaushe kikayi wannan Uban Aikin bansani ba,"




Bud'e bayan motar yayi yasaka yadawo yabud'e mata, 




"Lokacin kafitane"




"Kidana Wahalanda kanki dayawa my Sugerty" yafad'a yana kashe mata ido d'aya



Dariya tayi tana fad'in "nidai banaso kadaina"




Shima shiga motar yayi sukafice maigadin yana d'aga Musu Hannu Tareda fatan Farincikinsu ya d'aure, 



Hon yayi Bakin tangamemen gate D'in gida Saida security ya tabbatarda shine kafin yabud'e Masa yana gaidasu, inda Akatanada Domin parking yatsaya yafito yana k'ok'arin zuwa Bud'emata yaga tafito d'an b'ata fuska yayi yace"bazaki Jira nazo inada Aikin nawa bane neman shiri fa nake tayarda komai zaiwuce"




Murmushi tayi tace"kada kadamu Shirin yagama shiryuwa ai tinda kasauya fatana kada sauyin yazama na wucen gadi"


Dariya yayi yana d'auko basket D'in "in sha Allah ma nacanza kenan yanzu Dai *AKAN AIKIN MIJINA* Nasamu Farinciki yafad'a Tareda kashe mata ido d'aya



Dariya kawai tayi tana karb'ar basket D'in tashiga ciki shikuwa yakoma inda ma Aikatan gidan suka soma gaisawa Tareda yimusu Ihsanin daya saba,




Da sallama tashiga parlour Kasancewar weeding yasa duka Ahalin gidan suka parlour Domin k'a idar gidance duk ran weekend k'arshen sati Sukan Had'u Ayi Raha da ciye da ciye



Yauma Hakan takama domin dukansu sunzo Wad'anda sukayi Auran Maza da matasansu sai nishad'i suke,



Ansa sallamar sukayi, Husna tace"Oyoyo Matar yaya ta iso fa Matar big brozzz"




"Zakiyi k'alk'alar dakyar idan yashigo kuka Arba da rawan kan naki"



Dariya suka saki dukansu, k'arasa shiga tayi tana murmushi kawai har k'asa taduk'a tagaida hajiya tareda Aje basket D'in




Ansawa tayi Tareda mata Sannu cikin kulawa,


Aikuwa suka sake suka Soma fira sosai dukansu,



Shigowa yayi Shima suka gaisa kafin yazauna yana danna wayarsa kawai halinsa na miskilanci yana nan lokaci lokaci Dai yakan Saka musu Baki ko yayi murmushi,





Abinci Suwaiba mai Aikin hajiya tasoma Ajemusu Nan K'asan carpet D'in Bud'ewa Hasima K'anwar Muhayseem tayi tace"to nidai bazan Jira kowaba Domin Uzurce nake"



"Dama ai Koda k'arin cikin yazo yataran dake dashen cikinki"



Dariya sukayi 



Tinda tabud'e Abincin takejin warin Abincin Sam garkin baimata ba shinkaface da go slow Tasha kayan lambu sai k'amshi ketashi Amma ita warin Abincin taji d'an kauda fuska tayi Domin Jin Wani Iri take kamar Zuciyarta tana hautsinawa, Amma ganin kowa yana k'ok'arin ci Hakan yasa tad'iba Ita tad'an Rintse ido Tareda Kai lomar bakinta kasa had'iyewa tayi Domin Wani Irin Amai yazo mata dasauri ta Mik'e Kasancewar gidan ba bak'onta bane Domin tinkan su soyayya tashiga tsakaninsu da Muhayseem take zuwa Domin Mahaifiyar Muhayseem K'awar Ummanta ce babba Wanda bawanda baisansu tareba, Hakan yasa tanufe toilet D'in k'asan parlour tasoma shek'a Amai har daganan parlour suna iya jiyo kakarin Aman nata,



Mik'ewa yayi da sauri Domin tuntashinta bisa idansa Maida wayarsa yayi Aljihunsa yabi bayanta Cikin sauri,





"A'a subhanallahi dama batada lafiya ne kuka zo," cewar hajiya



Taranda ita yayi tana Aman sosai Abun tausayi duk tawani fayau, rik'eta yayi Saida tagama yana mata Sannu Saida tagama yataimaka mata tawanke bakinta yarik'ota suka fito duk tana k'ok'arin bari jikinsa Amma yarik'eta Sosai Domin shi baiga Wanda zaiji kunya ba gurin,



Sauke idanuwansu sukayi k'asa suka soma dariya Tareda gulmarsu



 Zaunar da ita kan kujeran Ahankali Kuma tazame ta kwanta tana Maida numfashi



Sannu suka shiga yimata



Hajiya tasake maimaita maganar"nace son batada lafiya kukazo saikace dole gakuma wani Aikin datayi,"




Fuskarshi da Alaman damuwa yace"Allah hajiya Sam batanunamin batada lafiya ba Kuma bangano ba dabazan bari tayi Aikin ba kuma bazamu zoba, "



Dubanta tayi Ahankali yace"make damunkine gafa jikinki yayi zafi"



Shuru yaji yakai Hannu yatab'ata Nan yagane bacci ya d'auke ta,



Afili yafurta "wai harkinsamu bacci Dear"




Itadai Hajiya kallo d'aya tamata fuskance yaron cikine da Ita,



Maida kallonsa gun hajiya yayi yace"mudai zamu wuce tinda Banda Kayan Aiki Nan muje hospital nadubata jikin nata sai k'ara zafi yake"





 "Oh big brozzz saikace ba likita ba jiduk yarda ka rud'e ai ko ba'a fad'a ba kasan Aunty tasamu k'aruwa ne fa," tak'arasa maganar tana dariya..........


41 to 50*



         ......kalonta yayi Tareda nazarin fuskarta Anan yasoma ganin Alamun ciki tareda Maida kallonsa yayi gun Hajiya itamad'in murmushi take Tareda cewa"Allah dai ya inganta Kuma Allah yaraba lafiya, basai na fad'amaka bindoka da k'a idaba tinda Aikin Kane kasan komai gameda zamansa ko fitarsa saidai na k'ara tinamaka da kakula da Ita sosai Allah yarabasu lafiya"




Da Ameen suka Ansa dukansu




Tajima tana baccin saidaga baya tatashi gurinsu Hasima


Akunyace dai tabar gidan,



Saida suka biya Asibiti yayi gwaji Aikuwa na Wata d'aya sosai yayi Murna sosai kulawa kuwa saita k'ara ninkuwa Domin indai gurin son yarane Muhayseem badama,..



  BAYAN WATA D'AYA



To ni Mujaheedah Matar Mlm Zan iya cewa cikin wata d'aya D'innan 


Unguludai Takoma gidanta nagado Hahaha hausace fa nayi,



Dr Muhayseem dai yasake Maida k'arfinsa da halinkalinsa gun Aikin sa,




Yanzuma Zaune take tarauka Uban tagumi Zuciyarta saifaman sak'e sak'e take Anya kuwa Muhayseem baya neman mata? Shine Abunda Zuciyarta keta mata rawa Akai,


Saidai duk Wani yanayi datake ciki takasa barin kowa yasani harda babbar k'awata Kuwa Yasmin Domin babu Abunda batasani ba kan Yasmin, k'awance Mai k'arfi yashiga Tsakaninsu bayan Abotar mazansu domin Yasmin Macce ce wayayya wadda batasan munafurci ba Kuma kaifi d'ayace lokuta da dama ma ita Muhseenarh ke tausar Yasmin kan zamansu da mijin nata domin Wani lokacin cewa take kawai yasaketa sai dai Muhseenarh takanyi mata fad'an hkn Tareda tunatarda ita sunzama d'ayafa tinda harda Yara biyu sukeda ga babbar Macce so tayi hak'uri watarana zai iya sauyawa,



Mik'ewa tayi tashiga band'akin Domin zafi tasoma ji yanzu cikinta yana wata biyu ne,


Zuciyarta cunkushe take gayawan tunanuka Hakan yasa tasaka Kai kawai cikin toilet D'in bako Addu'a Kanta Kuma babu d'ankwali, inda famfom toilet D'in tanufa takunna idanuwanta rufe suke Tara Hannu kawai tayi suna zuwa tawatsa kan fuskarta, Wani Iri Tareda k'asni taji da sauri tabud'e idanuwanta Tareda kallon fuskarta A mirror D'inda ke toilet D'in saidai mezata gani? Jini tagani kanfuskarta da sauri takalle famfom tabbas jini kefita A famfom Amaimakon ruwa, Sosai ta tsorata Tareda soma jabaya tana k'ara goge fuskarta k'ok'arin juyawa tayi tabar toilet D'in cikin wata kalan murya Mai Amo da sauti taji Ankira sunanta"Muhseenarhhhhh" sunan Akakira Tareda ja cikin firgici da mutuwar jiki tawaigo bayanta idanta suka fad'a kan madubin dake Band'akin Wani hayak'i yasoma bayyana ciki fuskarsa rufe da dogon gashin kasansa kamar Wani balarabe ammafa duka hayak'ine, 

Tsintar kanta tayi da kasa Addu'a saboda tsabar tsorata jikinta sai rawa yake takasa yin gaba Kuma takasa matsawa baya, 



Dagacikin madubin yayi magana cikin muryarsa maisaukarda ciwon kai da mutuwar jiki ga Bil'adama yace"Kind'auka zan iya Rabuwa Dake ne ganin wata biyu banziyarce kiba, bawai na manta da bibiyarki bane kawai saboda mijinki yasoma Zama Tareda ke shiyasa nabarki Domin inada kishi kuma banason Aikata kisa bayan hakan mijinki yanada tsari Mai k'arfi bama wannan ba, bana ziyartarkine idan mijinki yana kusa saboda bana buk'atar kowa yasan Ina Tareda ke, kawai inason zama taredake gakida Kyauuu...." Yak'arasa maganar yana k'ok'arin tab'ata 



Ganin hannunsa yak'ara tsawo har yazo kanjikinta yasa takurma Wani ihu Tareda yunk'urin matsawa saidai cikin rashin sa'a santsi yakwasheta jikake timmm ta fad'i k'asa cikinta yabugu da bahon wankan Dake toilet D'in k'aran Azaba tasake saki take jini ya b'alle mata Dagan Kuma batasake sanin Ina Kanta yakeba,



Murmushi Aljanin yasaki Tareda fad'in *"AKAN AIKIN MIJINA* yab'ace b'attt





"Eh yanzu haka nafito gidanta zani Ina driving ne Auntie kubra bari na k'arasa idan naje saina mata Magana kan kinkirata bata d'auka ba"





"Ok saikin sauka Amma ki kirani dakanki saiki bani ita Muyi magana Dan wllh gabana fad'uwar yake bansan dalili ba"




"Bakomai Auntie tana lafiya ma in sha Allah, Amma danaje zankiraki"




"Okay wllh yatsare inajiranki" 



 

"To auntie"

k'ittt takashe Kiran Tareda Maida hankalita kan titi itama tana mamaki kwana 2 ko online tadaina ganinta,



Batajawani dogon lokaci ba ta iso gidan Saida tayi hong sosai kafin baba Audu yazo ya Bud'e ganinsa kamar firgice yasa bayan tashiga tatsaya Tareda sauke glass D'in motar tace"Waiko lafiya baba"?




Sale ne ya k'araso gurin tareda cafe zancen yace"Inafa lafiya Hajiya ce tasaki ihu kusan sau 2 saidai bamu sakejin motsintaba"





"Subhanallahi mijin nata baya gidane to meke faruwane,"?





"Wllh bamusani ba Kuma Kinga baiyuwa mushiga bayanan yana gurin Aikinsa,"



K'ok'arin fitowa motar take cikin tashin hankali tace"Amma shine Baku kirashi ba"





"To ai Hajiya ko Ankirashi baya d'auka Musamman idan yana gurin Aikinsa ne"



Dogon tsaki taje tace"wllh Allah waddaran wannan K'addararren Aikin nasu, Ace *AKAN AIKIN MIJINA* nafad'a halaka shi ko Ajikinsa"


Tak'arasa maganar cikin masifa tana shiga gidan babu kowa parlour Hakan yasa tashiga shiga kwad'amata kira tana bincika d'akunan Shuru bata Hakan yasa tashiga toilet D'in Anan tayi Arba da ita k'asa yashe kwance jini yana bin k'afafuwanta batako motsi, K'aramin ihu tasaki Wanda yajanyo hankalinsa yasa babu shiri suka shigasuma ganinta Hakan suma yabasu tsoro,


 


Baba Audu ne yace"Akaita Asibiti fa kamar tana zubda jini sosai," 


Sai A lokacin hankalin Yasmin yadawo jikinta yasa tace"kutaimakamin to mukaita mota"

Dataimakonsu suka sakata mota ganin duk ta rud'e yasa sale yaja motar suka nufe Asibiti............




Page 51 to 60*




......... Asibitinda suke Aiki sale yakaisu suna zuwa kuwa Emergency ganin jinin yana zuba iya tashin Hankali Yasmin tashiga Musamman ganin jinin baidaina zuba ba, ciki sukayi da ita suka soma bata taimakon gaggawa, yawo tafara Agurin tana share hawaye, 



 " Amma madam maizai hana kinemeshi tinda naga Nan yake Aikin"



Sai Alokacin tatuna harda fa Faisal Nan yake, juyawa tayi tanufe office D'insa saidai office D'in rufe, security Dake tsaron Bakin k'ofar yace"Madam basanan fa sunfita Sallah"



Batace komai ba tajuya motar tabud'e ta d'auke wayarta dariyar Kiran faisal saidai ganin missed barkatai daga Auntie kubra kafinma tayi Wani yunk'urin Wani Kiran yasake shigowa tad'auka duk Afirgice take tace"wllh Auntie kubra babu lafiya cikin mugun yanayi nasameta duka hankalina tashe yake shiyasa bankira kiba"




 Mik'ewa tsaye auntie kubra tayi Cikin dabircewa tace"Meke faruwa da ita? wane hali take ciki yanzu? Ina shi mijin nata Dr Muhayseem D'in,"? 



Batasamu damar Ansamata tanbayoyin ba Sale yanufota da sauri yana fad'in"wai Dan Allah bakida number shine ki kirashi sunce dole saisunga mijinta Kuma wai suna buk'atar kijini Domin tasamu miscarriage,"





"Miscarriage!? Wai cikin shine yazube,"? 



"Haka sukace wllh"




"Nashiga Ukku kinji Auntie kubra wai cikin yazube tayi miscarriage "



"Subhanallah innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn"


Shine kawai Abunda auntie kubra take maimatawa Tareda zama tana dafe kanta,




Yasmin kuwa dama tadatse Kiran tasoma kiran Faisal Saida takusa katsewa yad'aga



Cikin mugun Haushinsu suduka tace"Idan kasamu lokaci saika fad'awa Shashan Abokin naka dama halinku d'aya saidai banbanci ku kad'an ne, ka fad'amasa idan zai iya gamunan Asibiti Muhseenarh babu lafiya Kuma Ana buk'atar jini sannan haryanzu babu likita Kanta" batajira Ansarsaba takashe wayar wllh haushi sukebata dukansu, k'ofar word D'in takoma





Cikin Damuwa yace"Madam ce Kuma tace suna Asibitin Nan takawo Madam D'inka babu lafiya"



Cikin tashin hankali yamik'e yafito baiko saurare Kiran nasaba yanufo cikin hospital D'in bayan gama sallarsu ne Faisal yajasa Siyan Dambun nama,



Dama babu nisa Sosai Hakan yasa take ya iso, baiko tsaya yin magana ba yashiga d'akin cikin tashin hankali, 




Drip kawai suka sakamata sukabarta Domin Basu biya dukan k'ud'in Aikin ba kuma Basu Bada jinin ba Hakan yasa sukabarta,




((Hunmm kad'an daga cikin halin ma'aikatan Asibiti kenan zuwa kansu doctor's D'in, Koda yake yanzu komai na k'ud'ine bawai Dan Allah ba tho Allah dai Yasa mudace....))


K'ok'arin treating d'inta yafara dakansa ganin Hakan yasa nursing D'in suka shiga taimaka masa jininsa yabada Akasamata Saida ganin komai yalafa kan yakoma gefe yazauna share gumi cikin tashin hankali da damuwa Domin kuwa cikin yariga yazube Kuma Hakan yasamune saboda yawan jinin da tazubar gashi batasamu taimako kan lokaci ba,




Ai Kuwa yafufe duka nursers D'in gurin da Fad'a kamar zaidakesu, Saida falsal yashiga lamarin tareda Basu umarnin barin gurin 



Zama yayi k'asa Tareda dafe kansa Domin juyamasa yake gashi jininda yabada bashiri yasa yakeganin jiri





"Kanatsu mana Dr kaimafa na buk'atar bed rest D'in saboda bada jinin cikin rashin shiri,"






D'aga masa Hannu kawai yayi Alamar yarabu dashi, shi K'ad'ai yasan yaya yakeji A Zuciyarsa na Rashin wannan cikin Domin yasaka ransa da soyayya ga Cikin gashi Kuma shine silar zubewar jikin nasa,..





"Waimeke faruwane ne naga kina had'a kaya" 




"Ina lafiya nakasa rik'e Amana inanan y'ar uwata tanacan tana wahala ni Nigeria nakeson komawa yanzu"





"Nigeria kuma Momyn Khairat? Kinfasan komai basai nagaya Miki ba Ina kowa Nigeria yanzu Babu Shiri ko booking tickets bamuyi ba Kuma babu shiri, waima meke faruwane wacce Irin wahala waya gayami Muhseenarh tana da damuwa,"





Hawaye tasoma"wllh Abban Khairat da matsala dama inajin Hakan Ajikina gameda ita sai yanzu Kuma nakejin tana Asibiti Kuma tasamu miscarriage nidai Amin duk Abunda za'ayi gaskiya Nigeria nakeson komawa inason ganin y'ar Uwata"




"To shikenan zakiji Amma bayanzu ba Amma kinatsu kifara kwantarda hankalinki kinji," lallashinta yasoma hardai yasamu ciyo Kanta ta hak'ura saidai tacigaba da Kira...





Bayan wasu A wanni Ahankali tashiga ware idanta komai yashiga dawo mata kamar yanzu cikin firgici tamik'e Zaune Tareda sakin k'ara,



Shigowa Yasmin tayi Cikin sauri tazo gefenta inda Dr Muhayseem dama yajima da rik'eta tinda yana d'akin tareda ita, rungumarta yayi yana bubbuga bayanta tareda mata Addu'a Ganin kamar bama Cikin hayyacinta takeba, sunma suna tofa mata Addu'ar harda Yasmin 


Saican tadawo daidai Kuma sai lokacin idanta ya sauka kan cikin nata bataji motsin komai ba Kuma bataga Cikinba,



Cikin sark'ewar murya tace"Muhayseem Ina cikina banji motsinsaba, Yasmin Wllh cikina baya motsi"




Matsawa baya Yasmin tayi tana hawaye




"Me Hakan kenufi yasmin kukan me kike? Meyasa baka bani Ansar tanbayana ba Muhayseem Ina cikina, kada dai kacemin narasa cikina,"? Tak'arasa maganar tana hawaye Sosai Tareda shafa cikin nata.



I


"Saidai Muyi hak'uri Muhseenarh Amma kinyi miscarriage"





"Innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn, cikin yazube fa"





"Kiyi hak'uri my dear K'addara ce Kuma...."

Yimin Shuru Muhayseem!! Tafad'a Cikin b'acin rai, tareda k'wace jikinta daga nasa tace"Kaine Sila wallahi Kaine silan zubewar cikin nawa Muhayseem Domin baka damu dani ba balantana kulawa *AKAN AIKIN MIJINA* narasa d'an cikina!!!......…...............



Page 61 to 70*




 ........Saurin kama hannuwanta yayi idanuwansa suna sauya kala Cikin rauni yace"wllh bansan Hakan zata faruba da banyi wannan sakacin ba kidaure kisake bani dama zan gyara kuskurena duka Dan Allah kiyi hak'uri kibar wannan matsayi sirri banason kowa yasan cewar *AKAN AIKIN MIJINKI* cikinki yazube kibani dama My Dear zan gyara zansauya," ganin damuwarsa k'arara yasaka guiwarta sanyayewa mata da Miji sai Allah balantana Zuciyar Macce rauni gareta sam bata iya riqo Hakan yasata sauka tayafe masa Kuma har lokacin takasa bayyana Abunda ke faruwa da ita Domin batasamu damar yin hkn ba,




Kwana 2 tak'ara tasamu sauk'i sosai sukadawo gida Hutu yad'auka gurin Aikinsa na sati 1 Badan komai ba Dan yakore laifinsa, harda iyayensa Basu jindad'i fitar Cikinba saidai babu Wanda yasan cewar *AKAN AIKIN MIJINTA* Abubuwan suke faruwa,. Dakansa ya yanka Musu ticket suka d'aga zuwa Canada sukakaiwa Auntie kubra ziyara Dan hankalinta yakwanta dakuma neman rufe bakinta Domin yasan Auntie kubra indai kan Muhseenarh ne to bata d'aga k'afa gakowa, Kwana 2 suka dawo taji dad'i sosai Kuma tasaki komai yawuce,




BAYAN WATA BIYU



HAUSAWA SUKACE MAI HALI BAYA BARIN HALINSA INKO YABARI SAIDAI IN AROSHI YAYI BANASHI BANE, Domin kuwa A yanzu canzawar dr hartakaiga Wani lokacin baya kwana gida dataso yin k'orafi kuwa zainuna tayi hak'uri komai zai sauya,



Cikin iKon Allah tasake samun Wani cikin haryakai sati 4 Amma baimasan tanada shi Domin bazama yakeba idanma yawaiwayeta to buk'atarsace tamotsa iya bincike tabbas Dr baya neman mata shiba mazinaci bane shiyasa Wani lokacin takan d'aga masa k'afa Kuma Allah yayita da hak'uri,

Cikin kwanankin da baya zaman kuwa Aljanin yasata gaba Yanzu yadaina fitowa da Kansa saidai Abubuwan tsoro dasuke bayyana gareta,




Tinda tatashi yau takejin babu dad'i wayarta tad'aga takirashi kusan 15 missed call's baid'agaba Aje wayar tayi tanajan tsaki Zuciyarta namata sak'e sak'e, mik'ewa tayi tanufe bedroom d'inta Domin takwanta saidai Abunda idanuwanta sukagani ne yasata mugun sizewa Tareda d'auke wuta na wucen gadi, Wasu manyan jemagu bak'ak'e wulik tagani cikeda da d'akin halittarsu wata Irin k'uri suka mata da idanuwana Tareda nufar inda take jabaya tasoma tana k'ok'arin fisgo duk wata Addu'a daga bakinta, Wata tsohuwace tukuf tabayyana gabanta b'ullum idanuwanta sunyi jawur kamar garwashi Hannu tasaka tashak'e wuyanta tareda d'agata sama Cikin b'acin rai tace"Kind'auka kece kawai kikasan Allah tareda Ambatan Allah? Kinyi kuskuren shiga gonarda bataki muzakiyi k'ok'arin tonawa Asiri,"


Idanuwanta sukafito k'wak'wala Domin shak'a bata wasa tayi mata, gashi ba mutum bace k'afafuwanta suna reto k'asa idanta suka rufewa tana k'ok'arin d'auke wuta gaba d'aya,




 "duk Wani Abu dake faruwa dake kada kizarge kowa face mijinki, komai yana faruwa ne badan komai ba sai *AKAN AIKIN MIJINKI* bazamu tab'a barin kisamu Kwanciyar hankalinba ko haihuwa dole kema kigirbe kad'an daga cikin laifin *AIKIN MIJINKI* 



Saketa yayi tafad'o k'asa tana buguwa ga Cikin nata K'aran wahala tasaki take yarikid'a yadawo Ainahin siffarsa ta Aljanu Mai ban tsoro Tareda sakin murmushi cikin kakkausar murya yace" *AKAN AIKIN MIJINA* nasake rasa cikina wannan karon Yara 2 kikayi b'ari babu Abunda yajamiki face *AKAN AIKIN MIJINKI!!* 


Jinmotsi yasa yab'ace b'attt



Itakuwa take tasume gurin



Shigowa d'akin yayi yanakiran ta Ganin halinda take ciki yasashi mugun tsorota Tareda d'aukarta Zuwa Asibiti wanna karon tasha wuya Sama da farko Domin Saida tayi kwana 3 tana Cikin suma,




"Sannu kin Farka meke Miki ciwon"?



D'auke idanuwanta tayi kansa batayi magana ba, Ayanzu ba iyazafin rasa cikin takeba Maganganun Aljanin suka shiga dawowa A k'wak'walwata "komai yana faruwa ne badan komai bace *AKAN AIKIN MIJINKI* Shin wai meke faruwane *AKAN AIKIN MIJINA!*? Tabbas yazama wajibi Kuma dole gareni Akan nashiga bincike gamida da tuhumar gaskiya *AKAN AIKIN MIJINA!!*


wannan karon ma b'oye yayi Dalilin zubewar cikin Amma Dai yasha fad'a gun hajiya yakan yak'ara kulawa da ita,


Itakuwa tamkar bataji zafin Abun ba Hakan tanuna saidai yanzu yaga sauyi Abubuwa dayawa gareta kiransa damuwa duk tadaina, Abunda baisani Bashine Yanzu tashirya tsaf Domin gano gaskiya gameda Aikinsa....

.....


Page 71 to 80* 



...........Sosai tasaka idanuwansa gameda motsinsa zuwa Aikinsa Amma Abun mamaki takasa samun hujjar da wannan Aljanin yake Wahalan da ita Kuma idan tayi yunk'urin fad'a saita kasa gashi Banda wahala da tsoro babu Abunda take tsinta Agidan k'arin takaicin kullum harkan Dr Muhayseem gaba gaba yake narashin bata Lokacinsa bata rasa Ciba ko sha balantana suntura saidai tarasa kulawa Sam babu Lokacinsa gareta k'ud'i ko Iko duka basuda Wani Mahimmanci ga Rayuwar Macce inbabu kulawa, 





Zaune take kamar kullum tarafka Uban tagumi saiga Yasmin



Hartashigo bataji taba Domin tayi nisa A duniyar tunaninta,

Zama tayi gefenta Tareda dafata tace"Haba Muhseenarh wannan damuwarfa yawan damuwa yakan Saka Mutum cikin hatsari Akwai cutuka dadama Wad'anda tunani yakan haifarwa d'an Adam, Muhseenarh wllh idan Wannan Auran yana cutardake kawai ki hak'ura Allah zaimiki zab'i mafi Alkhairy Amma wannan damuwar babu Abunda zata haifarmiki dashi face illa babba,"




   Ajiyar Zuciya tasauke tace"Nasani mom Khairat Amma banda solution dole nayi tunanin Domin shine kawai Abunda nake naji sanyi a Zuciyata, Yasmin Ina mamaki irin soyayya da kulawa da Dr Muhayseem yanunamin kafin Aure ko yanzu wasu lokutan Idan matsala tafaru dani yakan bani kulawa sosai Amma haka kawai dai babu yafifita Aikinsa sama da komai, wllh ni Yanzu har tsoro yakeban Anya dakwai gaskiya gamedashi kuwa,"?





Hunmm"Muhseenarh Kenan kinfi kowa sanin halin Dr Muhayseem Ayanzu Domin kinsan Abubuwanda ko Mahaifiyarsa bata sannu ba Amma kinsan meye matsalar? Shi namiji bashida tabbas duk saninda kika masa toko wanne lokaci zuwa dak'ik'a wallahi zai iya canzawa sannan soyyar cikin gida daban Wadda kukayi waje Daban, Kuma kinsan Allah bawai Ina miki mugun fata bane Amma wallahi muddin kikacigaba da Saka damuwa gameda namiji to wllh Zuciyarki zata tarwatse ne Abanza, indai Zaki cigaba da damuwa to wallahi Nan Bada jimawa ba *AKAN AIKIN MIJINKI* zakiyi mutuwar kasko, Kuma za'a rubutaki daga cikin tarihi Duniya cewar ga wadda tahalaka *AKAN AIKIN MIJINTA*






juyowa tayi Tareda kama hannuwanta tace"Yasmin ki fad'amun gaskiya kinsan banida k'awa saike kinsani su Abbana sunyi tafiya banason Susan banada natsuwa wllh saboda gudun damuwarsu, Auntie kubra itace komai na saidangin Mahaifiyata banason Susan damuwata Kuma bason auntie kubra tasani Domin zata iya shiga damuwa Kuma kinsan halin auntie kubra batada hak'uri tanajin Labarin wllh zata yanke Hukuncin Rabuwa Kuma wllh saita fad'awa su Umma, Dan Allah meye shawaran da zakiban, Kuma Anya Baki ganin Dr Muhayseem yana neman mata ne,"? 





"Nima yana dagacikin Abunda yake d'auremin Kai gameda shi, to baka shaidar namiji dai amma Sam Dr Muhayseem baiyi kama da mazinataba to saidai indai neman matan ne lalle nasan Mijina Dr Faisal wllh yanabin Mata wllh nasani Muhseenarh Amma Kuma yana ban lokacinsa gaskiya saidai mata kam Hunm ba'a magana duk da yana b'oyemin Amma wllh ninasan yanayi Kuma kinsan indai Akacemiki lecture's Malaman boko zuwa Malaman Asibiti likitoci sojoji to Wad'annan bayyane yake da shegen neman matan tsiya Kuma bance suka sunayi ba Amma wasu kam ba'a magana so saimadai Wad'anda Allah yatsare sune kawai basuyi amma masuyin sunyi yawa Wllh, Amma kada kadidamu zan k'ara Saka ido tareda tsananta bincike kan lamarin, Amma fa kidaina damuwar,"





"Kinsan me? Kobayan wannan dakwai Wani k'ullin Kuma wllh gidannan dakwai Aljanu Taredashi suna masifar tsoratar Dani Musamman idan baya gida, Yasmin inacikin jarabtuwa nidai wllh inajin hak'ura da Auran duka Wllhi Nagaji da halinsa gakuma d'ayan matsalan Iskan danake fuskanta"





"Iska Kuma Muhseenarh? Wai kina nufin A gidannan kina ganin Aljanu,"?





"Sosai Ada iya tsoratarwa kawai Amma Yanzu harbayyana yake gareni Kuma namiji ne saidai babu kalan siffarda baya zuwarmin da ita yana wahalar Dani sosai duk Wani cikina yanada Saka Hannu Shima gurin zubewarsa Kuma k'arin tashin hankali ya fad'amun cewar babu Abunda yajefani cikin matsalan face *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Gane Meye Abunda yake nufin cewar *AKAN AIKIN MIJINA* Shima yake Azabatarda ni, shine nake tunanin Koda wani Abu mara kyau Wanda Dr Muhayseem ya tab'a Aikata Wanda yasa Yanzu nima nake girba wannan Wahalan, nidai *AKAN AIKIN MIJINA* wllh Ina nadamar soyayya dashi dama Auransa Dani Badan komai ba saidai Dan *AKAN AIKIN MIJINA*"

Hawaye tasoma zubarwa





"Kinga kiyi hak'uri komai zai wuce in sha Allah, Amma kidaina zarginsa duk da bansan meye A k'asa ba Amma bana tunanin Wani mugun Aiki daga garesa, saidai kawai nafi zargin Ansamun matsalan ne badan komai ba Saidan kawai Rashin kulawarshi gareki dakuma sakacin dakika fara na Ibada Muhseenarh damuwar *AKAN AIKIN MIJINKI* itace tajefa Miki wannan sakacin da lalacin dole ki farka Muhseenarh kada kibari *AKAN AIKIN MIJINKI* kihalaka Abanza, Kuma zanyiwa K'anen magana kinsan yana Harka Irin ta jinnu Saidai yanzu baya Nan yatafi Umara saidai dai inyadawo Nan Bada jimawa ba, Amma kidage da Addu'a da ibada Allah zaikawo mafita,"



"Shikenan Mom Khairat zan kula ngd sosai, Allah yabar zumunci"




Sunjima suna fira kafin tawuce,



Yaudai tasaka Aranta zata k'ara yawan ibadarta, domin kariya wakanta,




Zaune yake office D'in wata Irin gigitacciyar Sha'awa yaji tana motsa masa, mik'ewa yayi da k'yar ya Lipton tareda lemon tsami yasha Amma Abanza banji Wani Sassauci ba lemon tsamin yasake sha hakanan yana b'ata fuska Amma Shima babu Abunda yamasa yasani sarai Basai Anfad'a masa Irin illanda yake Shirin jawa kansa, 


Shigowa Faisal yayi yana fad'in"Dr nifa kasan bana iya Kwanciya Asibitinnan Wllh Kuma kafi kowa sanin idanuwan Madam suna kaina motsi K'ad'an zatace Ina Tareda watane Dan tafara tagoni yanzu tagane *AKAN AIKINA* Ina cin Amanarta bayan idanta to Kuma kasan waye k'anen babanta idan yagano sunana sorry shiyasa nakeson janye hankalinta daga kaina saina cigaba da tsula tsiyata lafiyata lauu *AKAN AIKINA* nasha Abuna wallahi,"



Jin baitanka masaba Kuma Bai d'ago Kansa ba yasa yamatsa kusadashi Tareda dukan teburin yace"are you okay Dr Muhayseem"



D'ago idanuwansa yayi ya kallesa sunyi jajir Kuma sunkoma k'anana,

Subhanallahi dama bakada lafiya ne? Meyafarune da......"?

Mak'ale sauran maganar yayi ganin Uban tulin lemon tsami



Ai Kuwa yarik'e ciki yadinga tintsira da dariya harda fad'uwa k'asa, dama Faisal gwanin dariyar k'etane, har Abun yasoma harzuk'a Dr Muhayseem


Cikin k'arfin Hali Yace"Meye Kuma Abun dariya? Kasani gaba kana dariya saikace Kaga Wani mahaukaci,"? Cikin hasala yak'arasa maganar





"Au Yi hak'uri nadaina, Kaine ai keda Abun dariya yanzu duka wannan Uban Kayan tsamin Acikinka kajuyeshi? Kai Dr Muhayseem kanason Azabtarda Rayuwar ka Wllh, kanada mata Amma saikayita Wahalanda Kanka itama ka wahalanda ita gakanan kamar Agogo sarkin Aikin kullum kana busy hartakaiga kana Neman illata taka lafiyan, Kai Alaji gawata shawara tinda dai kana busy Mezai hana kad'auke shawarata Yau tinda dai matan Nan suma sunayinka kanada farinjini garesu Kuma kanada k'ud'i Kai koba ko sisi ninasan dakwai matanda Inka kirasu Wllh dagudu zasu bika kawai kasamu d'aya karage zafi,"





 Wata uwar harara yabanka masa yace"Kaga nayi kamada mazinatane? Ko ka d'auka bansan illa ko Hukuncin zina bane? Duk lalacewar da zanyi bazan Aikata zinaba kaima fatan shiriya nake Maka, Kuma kada kasake maimaita min Irin wannan k'azamar shawaran, Mtsww matsamin nawuce" mik'ewa yayi yabar office D'in yana d'an cije lip's d'insa,



Ai Kuwa Dr Faisal yasake fashewa da wata uwar dariya,



Yanajinsa Bai kulasaba har yakai inda motarsa take yashiga yanufe gidansa Agigice..............





.........Saida tayi Alwala tayi sallah kafin takwanta, Ahankali bacci yasoma saceta,



Hong yashiga dannawa Ad'an firgice baba Audu yazo yaduba Ganin motarsace yasa yabud'e cikeda mamakin ganinsa yanzu, yana Bud'emasa yashiga baiko Aje motar inda Akasaba Ajewaba yafito bako gaisuwarda Akasaba yashige gidan parlour tsaf kamar ko yaushe, direct d'akinta yanufa yaci sa'a kuwa Bud'e k'ofar take yashiga, cikin baccinta tajishi kamar mafalki saurin Bud'e idanuwanta tayi tana k'ok'arin mik'ewa, saiya k'ara matseta jikinsa yana fad'in"relax my Love nine Mijinki ne"




"Meya dawo Kai yanzu kana lafiya Kuwa Kaga ni bana buk'ata karabu Dani," tak'arasa maganar tana fisge jikinta tamik'e tsaye 




"Kiyi ha...k'u..ri ba...zan..iya" saikuma yakasa k'arasa Maganar jikinsa yad'auki rawa idanuwansa yana Wani kafewa,



Tsoro taji domin bata tab'a Ganinsa cikin Irin wannan yanayin ba dukda tasan idan yana cikin halin buk'atuwa Musamman idan yakai geji yakan soma ficewa hayyacinsa, 


Baiwar Allah dakanta tarage Kayan jikinta takwanta tareda rungumarsa, kamar Wani mayunwacin Zaki haka yakasance,


Ai kam taji Ajikinta na kwana biyu Basu Had'u ba,



Washe gari kuwa cikin Farinciki suka tashi dukansu kamar babu wata damuwa tsakaninsu,






"Wai kina nufin Wannan karonma yasake kub'uta daga tarkoki Zeeza,"?



 

"Hunm shegen wayau ne dashi dakuma taka tsantsan tahanyar kare mutuncinsa,"





"Ai na fad'amiki indai kinason galaba kanshi tofa lalle dole saikin fara rabashi da matarsa wannan tsinanniyar tatare komai"





"Amma fa nayi Aiki Kanta dan yanzu haka dakwai Aljaninda nasa Akaturama shegiya kenaji mafa Anci sau 2 tanayin miscarriage Kuma inada tabbacin yanada nasaba da wannan Aljanin domin banason Abari tahaihu sonake uwarsa tagaji tace dole saiya saketa Kinga baida zab'i Anan dole ya Aureni,"




"Amma taya kuka samu damar shigarda Aljani jikinta bayan nasan bata wasa da ibada,"?




Hunmmmm"habadai dai Aliya kinmanta wacece Zeeza? Babu Abunda bazan iyaba indai Akan cikar burina ne, Shakera 5 fa natab'a inason Mallakar Dr Muhayseem Amma cikin kwana d'aya rak wannan shegiyar ta b'atamun komai Kuma harkike tunanin nabarta wllh bazan barta samu natsuwa Kuma dakanta zata nemi saki Dan Ubanta Domin Dr Muhayseem nawane ni kad'ai, Waya gayamiki Aljanin jikinta yake? Ina ko Alama kawai Agidan Akaturasa Dan yadinga zuwa yana tsoratarda ita Gamida razani, dama banson yashiga jikinta Domin idan yashiga jikinta cikin sauk'i Asirina zaitonu Amma tahakan bawanda zaigano Domin Koda Za'aje gidan karatu baza'a samu Aljanin ba, boka yasamu damar turashi saboda damuwa *AKAN AIKIN MIJINTA*"





Jinjina Kai Aliya tayi kantace"bakida dama Zeeza, Amma Kuma kinsan cewar Dr Muhayseem baida lokacin komai saina AIKINSA har wadda yakeso yakasa kulawa da ita badan komai ba Saidan *AKAN AIKINSA* Amma kike tunanin Auransa da wannan Halin nasa,"?





Hahahahah"To ai wannan baidameni ba idanma baibani kulawa ba zannemota dakaina Ai, itace Wahalalliya dahar zata kame Kanta bayan tasan shi sakarai ne baya bata kulawa duka *AKAN AIKINSA* Kuma tajure komai, Allah sarki Muhseenarh saidai tayi kuka tace" *AKAN AIKIN MIJINA* Narasa Farinciki, *AKAN AIKIN MIJINA* narasa cikina narasa gudan jinina" 





Hahahah suka d'auke dariya gamida shewa dukansu...




BAYAN SHEKARA D'AYA



Zaune take cikinta yasoma mata nauyi domin yanzu yakai kusan wata 5, murna ganin cikin yatsaya, harda Auntie kubra taso tadawo gurinta Amma yak'ibari Kuma su Umma sundawo Nigerian suka Saka Baki Hakan yasa dole Auntie kubra tabarta Amma Yasmin tana yawan zuwa dubata hakama K'anwarsa Husna harda wata dattijuwa Hajiya tabata dakanta domin kulawa da ita domin Atunaninsu yarintace tasaka cikin yake fita,



Zaune take tareda Inna laraba suna tab'a fira tamik'e tashiga bedroom d'inta Domin takwanta,



Azaman Inna laraba gidan tafuskance Dr Muhayseem baicika kulawa da itaba shidai Aikinsa, girgiza Kai kawai tayi tafeda tausayinta,




Tana shiga d'akinta tashiga toilet Domin watsa ruwa kamar yarda tasaba, idanta takai kan madubin toilet D'in Wani bak'in maciji Mummuna ya bayyana Baki wulik tareda fitowa yanufota kansa yasoma rik'id'a yadawo na Mutum, jabaya tafara tana k'ok'arin ficewa Amma Ina cikin sauri macijin yayi sufa yakai Bakin k'ofar tareda nad'e handle D'in k'ofar yasoma Mik'ewa tsaye,




"Innalillahi wa Inna ilaihin Rajiunn Inna Inna Inna laraba! Wani yazo yataimakeni mana bakowa ne Anan"





Wata k'atuwar murya mara dad'in saurare Macijin yasoma dariya kansa yana Rabuwa izuwa gida biyu d'aya macijin d'ayan siffar hayak'in Aljanin,



"Kincika taurin Kai Muhseenarh kinkasa d'aukar mataki kin kasa samawa kanki lafiya dama cikinki, kindage da nuna soyayya bayan shi ko kulawa Dake yakasa baisan komai ba sai AIKINSA kawai kawai, Amma kingane kizauna dashi kina cutuwa kina bak'inciki kina fad'in *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Farinciki, to Baki gama rasa Farinciki ba domin ko yanzu wannan cikin saikin rasahi *AKAN AIKIN MIJINKI* ke nangaba kad'an kema Zaki mutu bakan komai basai *AKAN AIKIN MIJINKI*, Hahahaha *AKAN AIKIN MIJINA* nasake rasa cikina" yak'arasa maganar yana babbaka dariya




Sosai take cikin tashin Hankali da tsoro duk ihunda take babu Wanda yake jinta,



Jelansa Macijin yasaka yadaketa Aciki da k'arfi Saida tayi baya tabugu da Bangon toilet d'inta, K'aran Azaba tasaki bata gama dawowa hayyacinta yasake Saka jelansa yad'agata masa yakoma sakota k'asa cikinta yasake buguwa da tayis D'in toilet D'in, wani K'aramin ihun Azaba tasaki idanuwanta suka soma lumshewa numfashinta yasoma guduwa, take jini ya b'alle mata babu gaggautawa yasoma fita, gefen goshinta yafashe hancinta da bakinta suka soma fidda jini suma, lek'ata Macijin yayi ganin bata numfashin yasa yab'ace b'attt Abunsa.....................


Page 91 to 98*



```SECOND TO THE LAST PAGE IN SHA ALLAH```




            ..........Da sallama Auntie kubra tashigo d'akin, Inna labara ce parlour ta Ansa mata tazauna suka shiga gaisawa cikin kulawa, dama Aunty kubra batada girman Kai Hakan yasa kamar tasan Inna laraba,



"Halan masu gidan basananne kece kawai Inna,"?





"Eh shidai Dr bayanan kinsan dama bazama yakeba to ita yanzu ma ba'a jima sosai ba tatashi Nan inda kika zauna tacemin zata mik'a tahuta, kinsan masu ciki basajin dad'in zama guri d'aya Musamman Yanzu daya fara girma dole taga canji kala kala,"






"Hakane kam Allah dai yarabasu lafiya, bari nashiga naganta batasan da zuwana ba bazata namata"




"Ameen Ameen, Ah to lalle tho ko yau munada Bak'i Ashe"




Tana dariya tashiga parlour da sallama Shuru zama gefen gadon tayi tana tunanin kota toilet ne? Ganin tajima yasa tanufe toilet d'in tad'an kara kunnenta jikin k'ofar waikotaji motsi Amma Shuru Hakan yasa tad'anyi nocking nanma Shuru, Hakan yasa tatura k'ofar tasaka Kanta ciki tana waige waige kwatsam idanuwanta suka fad'a kanta tana yashe k'asa bako Alamar Rai tareda ita jini yana tazuba harda gudajinsa tak'asan k'afafuwanta fuskarta takumbura jinin yana zuba tabakinta,


K'aramin k'ara tasake tareda fad'in"Innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn, Muhseenarh! Muhseenarh!! Muhseenarh!!!" Tafad'a tana k'ok'arin janyota jikinta tana kuka," 



Jiyo ihun nata yasaka su Inna da sale sukashigo d'akin toilet D'in kaitsaye sukanganta rumega Ida tana kuka sosai,




"Innalillahi wa Inna ilaihin rajiunn, Kai Amma Anyi tsinannen Miji Wllh gashi ko Yanzu *AKAN AIKIN MIJINTA* tasake shiga Wani hatsari,"




Tsaida kukanta Auntie kubra tayi tareda juyowa takallesa cikin mamaki tace"dama *AKAN AIKIN MIJINTA* take fuskantar hatsuruka Irin Wad'annan,"





"Sosai ma Kuwa wallahi dama ni Ina jiran randa zansamu dama naga Wani jininta nafad'a masa gaskiya Kai Koda nayi yunk'urin fad'ar gaskiya baba Audu shike Hanani wai kada nashiga tsakanin ma Aurata, Amma Wallahi nidai tinda nazo gidan Nan bata tab'a shafe sati d'aya da Farinciki ba, koda yayi sanyi kamar zaidaina to wallahi kwanciyar d'aukar Rai yayi gameda mata wayo datagama warwarewa zaisake komawa y'ar gidan jiya, Indai *AKAN AIKINSA* ne to bazaka tab'a Gane kansaba, baida lokacin kowa komai saina *AIKINSA* Shidai *AIKINSA* shine Rayuwarsa, ko cikin farko daya zube Wallahi babu Wani dalili face *AKAN AIKIN MIJINTA*"




Wata nannauyar Ajiyar Zuciya tasauke Mai d'auke da zafi, "Kutaimakamin mukaita Asibiti," 



Dataimakon Inna laraba sukakaita Asibiti wannan karon wata Asibitin daban takaita Emergency Akashiga da ita, duk iya k'ok'arin sunkasa tsaida jinin numfashin natama yasaka dawowa, dole Auntie kubra takira su Umma cikin k'ank'anen lokaci suka iso ganin Irin yanayinda take ciki naruwa da mutuwa yasa Abba yasoma cuku cukun yankamusu ticket zuwa birnin New York, Sale ne dakansa yakira su hajiya ya fad'amusu, Hajiya takira Dr saidai wayar bata Shigaba dole suka nufo Asibitin, Wani Dr yafito yana sharce gumi yace"Jikinta yayi tsanani Sosai dakwai buk'atar Ayimata theater Kuma dakwai na'urori na Musamman da za'a buk'ata Kuma wannan Aikin yanada hatsari yana buk'atar k'warewa dole dai sai Annemo Dr Muhayseem Domin shine da k'ware tawannan gefen,"





"Babu buk'atarshi Anan zamu d'auketa daganan zuwa k'asar waje nasan Acan za'ayi solving matsalar" cewar Aunty kubra cikin fushi



Ko kula su hajiya Dake magana batayi ba,





"Wai to meyayi zafi kubra dazakice ba'anemansa mijinta nefa kobayan zamansa Dr D'in yafi kowa Hake Kanta"





"Au haba shindama yana da hakke akanta to ai bansani bane tinda banga hakken nata daya sauke ba, yana da hakke ita Batadashi kansa Kenan Hajiya,"




"Taya Zaki fad'i Hakan kubra ai kinfi kowa sani kan Miji nada hakke kan matarsa hakanma matar tanadashi kan mijin,"





"Masha Allah gwanda dakika fad'a dakanki cewar itama tanada hakke kansa to ki fad'amun wane hanke nata ya sauke, Banda Wahala da Bak'inciki metasamu Agidan Auran nashi, Mutum baisan komai ba sai *AIKINSA* kawai yasawa neman duniya gaba yana neman kashe Muna ita, badan komai ba sai *AKAN AIKINSA* saunawa tayin miscarriage? Kuma ba silar kowaba sai shi Mijin nata Dr Muhayseem Kuma babu Wani dalili face *AKAN AIKINSA* shikenan ita haka zata k'are cikin zubewar ciki da K'unci da Bak'inciki tana fad'in cewar *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Farinciki to wllh bazaiyu ba idan Ada Anyi bananan to Wllh yanzu nadawo Kuma dole yasake ta bazaiyu tazama Macce tafarko daza'a buga kan jarida cewar *AKAN AIKIN MIJINA* narasa Farinciki hartakaiga rasa Rayuwa, inda Wani ne ai da yanzu yazo, kira nawa Ana masa daga k'arshe ai kashe wayarsa yayi badan komai ba saidai yanuna cewar *AKAN AIKINSA* zai iya barin komai to badamuba wllh badamuba Hajiya,"






"Kubra yau nike kallo idona kike fad'amun maganganu Hakan bako tuna surukantaka haba ai yakamata kisan da K'addara"





*Amma ko kinbani mamaki K'addara fa kice to idan K'addara ce kijira ta fad'a kan sauran y'ay'anki mata Kinga kinada kan d'auka saiki d'auka maganar kuwa dole na fad'amiki domin d'an kuka shike jawa Uwarsa jifa, inma banda k'in gaskiya ga komai Bayyane Amma kikasa bin gaskiya,"





"Ke Aunty kubra ya isheki wllh bazaiyu kisaka Mahaifiyarmu gaba kina gaya mata Magana ba Kuma kina k'ok'arin muzanta d'an Uwanmu gabanmu ba," cewar hafsat,"





"To K'aramar kunya zokidakeni nace kizo kidakeni tanan zansan kincika mara kunya, Kuma...."





"Ya isa haka kubra ta lafiyarta Yakamata mubi bawai ta Wannan hayaniyar ba muje kawai," mama tafad'a tana kuka Tareda bin bayan nurse's d'inda suka gunguro Muhseenarh kan gadon kamar gawa zuwa mota Domin kaita waje, duk rigimar da Ake dai Abbanta baya gurin Domin yaje Yanko ticket,



Motar Akasata suka wuce airport direct Basu jima ba kuwa Abunka da Manya take jirginsu ya d'aga Kuma already Abba yayi magana da Dr Sabeer dake can new York D'in,




Su hajiya kuwa jiki ba k'wari Musamman ganin halinda Muhseenarh take suka nufo waje tanan suka Had'u da Yasmin tana k'ok'arin shiga tsayawa tayi tana tanbayarsu lafiya, Husna ce Dake kuka ta tsaya tabata labarin sunwuce da ita,





"Ya sallamm Allah kaceci wannan baiwar taka kabata iKon cinye wannan Jarabawar tata,"



Dawowa baya Hajiya tayi tace"Yasmin nasan kinsan Muhseenarh sosai tinda batada wata k'awa sama Dake shin da gaskene Dr Muhayseem baidamu da itaba sai *AIKINSA*? Shin dagaske ne *AKAN AIKIN MIJINTA* tarasa cikin nata har sau 2 kuma gana 3 cikin hatsari,"?





 "Sosai Kuwa hajiya wllh babu k'arya cikin lamarin, Muhseenarh tanada da hak'uri fiyeda tunanin Mai tunanin bata fad'awa kowa damuwarta nikaina saidaga baya na fuskance Hakan dakuma Gaskiyarda nasamu gurin sale driver d'insu wallahi Hajiya Dr Muhayseem yana cutarda Muhseenarh bakan komai ba Kuma sai *AKAN AIKINSA*, tana fama da Bak'inciki dama damuwa duka *AKAN AIKIN MIJINTA* yanzu gashi tasake fad'awa wata wahalar duka *AKAN AIKIN MIJINA* Kuma Aljanu sunsami damar shafarta sukansu sun fad'a mata sunsami damarne *AKAN AIKIN MIJINTA*"


Jirine yasoma d'aukar Hajiya Saida suka rik'eta sosai tashiga damuwa rud'u gamida Bak'inciki sai yanzu take ganin lalle kubra batayi laifiba sune keda laifin, 


Gida suka koma duka sukayi jungun har daddy daya dawo yasami labarin ai Kuwa yadinga fad'a wasudukansu Kuma yacigaba da Kiran Dr Muhayseem Bai d'aga ba ransa yak'ara hasala,




Dr Muhayseem kuwa yana d'akin theater lokacin yana fitowa kuwa yashiga toilet bayan yafito yasamu guri yad'an kwanta Domin kansa ke ciwo gawani fad'uwar gaba dayakeji, sai kusan yamma yad'uke wayar daniyar kira ai Kuwa yaga missed call barkatai ba Wanda Yafi d'aga masa Hankali kamar Kiran daddy da Aunty kubra, baigama nazarin wazaikiraba Kiran Daddy yasake shigowa, Cikin fad'anda baisan Daddy yanadashi ba Yace"idan Kaga dama Kaga zaka iya barin Aikin kafito saikazo yanzu inason ganinka yanzu idan Kuwa Banda darajar Aikinka yafi Maka to kayi zamanka," yana gama fad'in maganar yakashe wayar ransa b'ace yake sosai,



Cikin tashin hankali yasauke wayar A Hannunsa yana kallo cike da mamaki dama tashin hankali Domin baitab'aba jiyo muryan Daddy cikin Irin Wannan fushin ba,


Cikeda tsoro yamik'e yashiga motar yanufe gida cikin tsoro dama fargaban Abunda zai tadda,




Yana shiga gidan Yatsaida motarsa yashiga da Sallama k'ara tsorata yayi ganinsu jungum jungum hajiya harda guntun hawayenta itada Inna laraba, Hakan yak'ara jefashi cikin wasi wasi,



Cikin k'arfin Hali Yace"lafiya? Meke faruwa,"?





"Ta Ina zakasan Abunda yake faruwa Saboda babu Abunda ke k'ima mutunci daraja sama da AIKINKA, sau nawa muna kiranka Amma saboda Aikin ka yafaye Maka Mahimmanci kak'i d'auka, Ashe wahalar da y'ar Mutane kake Badan komai ba sai *AKAN AIKINKA* k'arin takaicin wai *AKAN AIKINKA* har ciki 2 yana zubewarsa yanzu Kuma gashi na 3 ma yafita Wanda itama bakada tabbacin zata Rayu ko zata Mutu, duka *AKAN AIKIN MIJINTA* tajure duka Wad'annan wahalhalun Anya Muhayseem kana Cikin Hankalinka Kuwa,"?





"Daddy banfahimce Maganar kaba kana nufin Muhseenarh Bada lafiya Yanzu haka,"?





"Rufe muna bani Shashashan banza Wanda baisan inda yake masa ciwo ba karon farko kasani kunyata gaban iyayenta da Y'ar Uwarta wllh kabani mamaki Ashe duk soyayyarda kake nunawa kana mata gabanmu duk ta k'aryace kaina da Kanka kake kashe yaranka ni wllh banga Amfanin wannan Bak'in Aikin nakaba Gashi yanzu duka *AKAN AIKINKA* karasa samun haihuwa, *AKAN AIKINKA* munsamu matsala da iyayen Matarka Abunda bantab'a ganiba cikin idan hajiya Jamila yau shinagani tsana, Abunda banyi tsammani ba Bud'e Bakin kubra ta fad'amun magana, duk kawaici Irin na bayin Allah Nan haka sukayi fushi suka d'auke y'ar su suka tafi Kuma duka *AKAN AIKINKA* ne Yanzu kota Rayu kota Mutu ba Wanda yasani Kuma saboda *AKAN AIKIN MIJINTA*," hajiya tak'arasa maganar tana sakin kuka,



Sosai jikinsa yayi sanyi tashin Hankalinsa yasake ninkuwa kenan yanzu iyayenta sune suka tafi da ita toma wane hali takeciki yanzu?




Zama yayi k'asa Tareda dafe Kansa,



Tsaki daddy yaja"yace baka gama shiga damuwa ba Indai *AKAN AIKINKA* ne Shashashan banza kawai




Baba lantana ce tahau bashi hak'uri da kwantar masa da Hankali Tareda k'warin guywa kan yaje ya kwanta gobe dasafe yabi bayansu,



Kamar yarda yaga Rana Hakan yaga dare Domin Bai runtsaba gaba d'aya cike yakeda nadama dama tsoron rasa matarsa zuwa cikinsa,



Tinda Assuba yatashi yashirya tareda yanka ticket baijira rakiyan kowaba yawuce airport k'arfe 7:30 am daidai jirginsa ya d'aga..........................



Page 99 to 100*


   ```FINAL FINAL FINAL FINAL FINAL FINAL FINAL PAGE IN SHA, ALHAMDULILLAH CIKIN IYAWAR UBANGIJI GASHI YAU NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN NAWA MAITAKEN AKAN AIKIN MIJINA, ABUNDA NAKESON KUFAHIMTA GAMEDA WANNAN LITTAFIN SHINE HAK'URI, DUK INDA MUTUM YY HAK'URI THO LALLE ZAISAMU SAKAMAKO MAIKYAU, KUMA HAK'URIN AKWAI INDA YADACE AYISHI KUMA AKWAI INDA INKAYISHI ZUNUBI ZAKA SAMU MAIKON LADA SABODA HAKA SAIMUN K'ARA GYARA RAYUWARMU, HAKA KUMA MAZAN KUDAINA D'AUKAR MAHIMMANCIN AIKINKU SAMA DA LOKACIN MATANKU BUDARENKU MACCE TAFI BUK'ATAR LOKACI KULAWA FARINCIKI SAMA DA KOMAI, HAKA KUMA MASU BIN MATAN KO KUNYI AUREN KO BAKUYI BA KUJI TSORON ALLAH KUDAINA DOMIN ZINA BASHICE, KUMA ALLAH YATANADE AZABA GA MAZA DAMA MATA, ALLAH KASA MUDACE 🤲, INDA NAYI DAIDAI A BUK D'IN ALLAH KABAN LADA INDA NAYI KUSKURE ALLAH KAYAFEMIN KUMA MASU KARATUN INASON KUYAFEMIN......```




 .....Acan kuwa dak'yar suka samu damar daidaito da numfashinta Tareda tsaida jinin, Nan take Kuma suka shiga da ita Sc domin sunfahimce Abunda yake cikinta yanada Rai, Abba shine yayi komai nasaka Hannu da biyan k'ud'in Dana haka take Ashiga da ita theater,




Dukansu Zaune suke jumgun suna mata Addu'ar kub'uta da Rayuwarta dukansu idan kadubesu zaka fahimce cikin tashin hankali suke shikanshi Abba dauriya kawai yake,






"Ai Hajiya yatafi tunda safen Yanzu haka inada tabbacin ya isa sauka," cewar Inna laraba





"Amma Hajiya yakamata Kuma kubi bayansa baidace Ace tana Cikin halin ciwo ba Kuma ace babu dangin mijinta ko d'aya natabba inmune wllh iyayenta zasu Kasance gurin Kuma Hajiya kinsan tanada kirki tana girmamaki Sosai ko yanzu Abunda yafaru tsakaninku da kubra b'acin Raine Kuma yaya shine yajanyo Hakan wllh batada laifi,"






"Hakane Husna kina da gaskiya ai nayo bucking ticket zuwa k'arfe 10:00am zamu tashi dagani sai Hajiya ai dole muje kodan gyara Abunda Yab'ata, kitashi kifara shiri nima shiryawa Zanyi,"



K'arfe 10:0 daidai suka isa Tareda Hawan jirgi suka nufecan cikeda fargabar taryarda zasu samu duk da basuda tabbacin inda suke Amma sunada tabbacin isa tinda har Dr Muhayseem yanacan,,.




Fitowa Dr Sabeer yayi tareda murmushi kan fuskarsa Abokin Dr Muhayseem ne sune kawai Basu saniba Amma Kusan tare sukayi degree d'insu na 3 Anan New York yaso yatsaya suyi Aiki tare Amma yakoma Nigeria,



Da sauri suka nufosa suna tanbayarsa yaya Ake ciki,? Murmushi yasake saki cikin haushen turanci yake fad'a musu"Alhamdulillah munyi Nasaran ceto Rayuwarta Kuma Alhamdulillah harda yaron cikinta munceta saidai inabaku hak'urin cewar d'ayan shi yajima da mutuwa Koda mukayi Aikin yamutu,"




"Dr dama kana nufin Y'an biyune Acikinta,"? Cewar Aunty kubra




"Sosai kuwa shikanshi saboda shine nasaman to saboda fad'uwarda tayi kansa tadanneshi hakan yasa yayi sanadiyar mutuwar d'ayan"




Jinjina Kai Abba yayi tareda fad'in "Alhamdulillah duk dahakan mungode Allah Ai," 




"Sosai ma Kuwa Koda Ansara yaran duka indai tana raye Ai Munyi Arziki balantana Ansamu d'aya Kai godiya ta tabba ga Allah"




"Wai Abba waketa kiranka tun jiya Hakan,"?




Murmushi yasaki"kubra sakin fad'a mijinta ne," yak'arasa maganar yana k'ok'arin daga Kiran




"Dan Allah Abba rabu dashi kada ka d'auka Mezai gayamaka to kada ka d'auka please,"





"A'a kubra ai yanada kyau nad'aga Ai haryanzu Akwai Alak'a tsakaninmu saboda shine MIJINTA baifa saketa ba Kuma ga k'aruwa Ansamu so dole na d'auka ai,"





"Ai Abba dole ma yasaketa dolensa" tak'arasa maganar cikin haushi datakaici




D'agawa Abba yayi cikin ladabinsa suka gaisa Nan yake tanbayarsa suna Ina gayanan yashigo fad'a masa Abba yayi, godiya yamasa Tareda kashe wayar,





"Dr zamu iya ganinta"



"Sosai ai tana d'akin hutu Amma Babu buk'atar hayaniya Kuma batare dukanku zaku shiga ba dole sai d'aya yafito d'ayan zaishiga Amma ganin yaron bayansu Domin Muna kan duba lafiyarsa shi,"





"To dr mungode"




"Umma ke kifara shiga" 




Duka sunganta sunfito hankalinsu kwance Yanzu tinda sunganta lafiya 



Kamar Wanda Aka cillo yashigo hankali tashe duk yarame yafige tamkar tare suke Ciwon bayama kan hayyacinsa yashigo karo sukaci dasu suna k'ok'arin fitowa tinda sunganta sukoma hotel mazauninsu saboda Akwai masu jinya babu buk'atar kowa yatsaya musu ka idar Asibitinsuce,




 

Risinawa yayi har k'asa yagaidasu cikin sakin fuska kamar ba komai Abba ya Ansa Umma ma ta Ansa saidai bakamar daba Auntie kubra kuwa d'auke Kanta tayi tana k'ok'arin fita,




"Abba Dan Allah Ayi hak'uri nasan nayi kuskure Amma bazan K'araba Dan Allah A yafemin"




"To ai Maganar kasake ko kar kasake Wannan kaita shafa bawai muba Mlm kadainama Wani sunkuyarda Kai kamar mutumin kirki Domin kayi na farko kayi na biyu kayi na uku Kuma to baka na hud'u wannan Shine k'arshe saboda haka mu bama k'aunar ganinka Nan kawai katashi kabar Nan, Kuma kayi gaggawar sake muna ita yanzu Nan Kuma saki uku muke buk'atar kayiwa Muhseenarh," Aunty kubra tayi maganar cikin haushi




Juyowa yayi cikin razana da tashi hankalin Jin kamar saki, Rabuwa fa Kenan, matsawa zuwa gareta yayi tareda durk'usawa k'asa Kamar Wani K'aramin yaro yace"Dan Allah Auntie kubra kidaina maganar Rabuwa wllh bazan iyaba Inason matata Wllh bazan iya Rabuwa da itaba, nasauya nadaina duka halin nawa bazan sake fifita Aikina sama da matata ba, bazan sake barin tashiga damuwa *AKAN AIKIN MIJINTA* nayi Muku Alk'awari Yanzu saidai tayi Farinciki *AKAN AIKIN MIJINTA* badai tayi Damuwa ba Dan Allah Abba Umma kumun Rai wllh bazan iya Rayuwa bataba nasan nayi kuskure Kuma nacutar da ita *AKAN AIKINA* Amma wllh bazan sakeba Dan Allah kuyi hak'uri"






"Kaga Dr Muhayseem kama daina Wahalan da yawun bakinka zuwa hawayenka Domin bazamu tausayamaka ba Domin kaima baka tausayawa Muhseenarh idan kamanta bari na tuna Maka sau d'aya biyu uku Muna baka damar canzawa Amma kak'i haka kasata Bak'inciki dama hararan cikinta Wanda har Yara 2 tayi b'ari badan komai ba Saidan *AKAN AIKINKA* haka tajure duk wata wahala da zafi kawai tazab'i Farinciki Kuma ta iya fad'awa duniya *AKAN AIKIN MIJINA* narasa cikina, Kai Muhayseem dole ma saika saketa Koda kuwa zaka Mutu ne kajecan ka k'arata *AKAN AIKINKA* Kai kad'ai Amma Bada jininnu ba,"





"Nashiga uku Dan Allah kubani dama naganta nasan tanaso bazata bari Hakan tafaru Abba nasan inada laifi Amma ku tausayamin kumun Uzuri Dan Allah,"






Shuru Abba yayi kafin yace"kabamu lokaci zamu zanta Akai" yana gama fad'in Hakan suka fice,


Komawa baya yayi zauna kan tayis D'in yana kuka sosai kamar K'aramin yaro, Ana cikin Hakan daddy yakirasa kan gasunan dole yaje yazo dasu direct hotel d'inda yasauka yakaisu Nan yake fad'a musu Yarda sukayi dasu,


Sosai sukaji tausayin d'an nasu suka soma lallashinsa,.....






"Inna ilaihin wa'inna ilaihin rajiunn menake Shirin gani haka Khairat dama Abunda kike Aikatawa kenan,"? 



Cikin tsananin tsoro tayi saurin jefarda wayarta tana jabaya kan gadon tana rawar baki takasa magana Domin Sam batasan da shigowar Abban nataba




Tsawa yadaka mata wadda tayi bala'in firgitata Domin tinda take bata tab'a ganin Irin fushinsa hakanba Kuma baitab'a yimata Koda fad'a ba balantana tsawa,




"Wai bazakiyi magana bane iyeee," ya k'arasa maganar yana d'auketa dawani gigitaccen Mari Wanda Saida tasaki fitsari A wando saboda tsabar zafin marin da razana,




*Idan Baki fad'amun gaskiya ba kasheki zanyi wallahi Domin bazan jure zama da mazinaciya A gidanaba, waye shi, yaushe kuka fara meya shiga tsakaninku, nace!!!," yasake daka mata tsawa yana shak'ar wuyanta,




Kakarin Wahala tasoma tana k'ok'arin k'wacewa takasa, 



Ganin dagaske Shirin kasheta yake Shirinyi yasaka Yasmin shigowa d'akin domin tunfarko duk Abunda suke kan indanta kawai ta k'yalesune Domin yasan tarbiyar y'arsa tagama gurb'ata dawo Irin tasa batareda sanin kowa ba,




Dak'yar tasamu tak'waceta hannunsa, itakuwa Khairat sulalewa tayi k'asa tafad'i tana faman tari da kukan wahala Domin tasha shak'ar ba kad'an ba,




"Wai meke damunka ne Abban Khairat Ina kabaro Hankalinka Shirin kisafa kake Kuma y'arka,"

Bagwanda tamutu kowama ya huta data b'atamun suna da tarbiyar gida, meye tarasa dahar zata zab'i bin Maza kinkuwa San wane yanayi nakamata,"?



Nunata yayi da yatsa yace"wllh duk Baki gayamin gaskiya ba kasheki zanyi A gidannan Zaki Bud'e Baki kiyi magana kosai nak'arasaki Anan," ya ida maganar cikin hargagi dayin k'ok'arin rik'ota


Ai da sauri tamik'e tayi bayan Ummanta tana cukuikuyeta tarik'eta Sosai tana kuka kuka





"Kinga My Love kibani yarinyar Domin wallahi bazan zabari tazama Ajalina ba kinsan yarda nakeji Araina kuwa,"?




Kallonsa kawai Yasmin tayi tareda murmushi, tace"wai dagaske Kanajin zafi lamarin,"?




"Haba Yasmin wace Magana kikeson fad'amun mara kan gado haka"





Hunmm"kawai dai mamaki ne Ace wai Kanajin zafi Yau saboda yau Abun yafad'a Kanka? Shin Kai kasan zafin da ni nakeji idan kaje kayi tarayya da wasu matan? Shin kasan Irin k'unarda iyayayen yaranda ka b'atawa Rayuwar sukashiga? Shin ni kasan Irin ciwo da Azabarda nake shiga idan kaje kayi ma'amala dawasu Matan nabanza waje? Hunm to Bari kaji nagaya maka ni danake Matarka Dama su iyayayen yaran zafinda mukaji wllh yaninka nasaka sau dubu, Kuma Kai baka isa kace y'ar zata tsallake daga tarkon zinaba wllh bazata tsallakeba,"





"Wai meke damunkine cinzarafina zakiyi gabanta ko nuna mata zakiyi Abunda ta Aikata daidai ne,"






"A'a ko kad'an ba hakan bane kawai Ina k'ok'arin fad'a Maka gaskiya ne Domin naga Alamar kajima da sauka kan hanyar gaskiya, ita kuwa zina bashice wllh duk Wanda Yaci dole yabiya Kuma Bari kaji ingaya Maka duk Uwa takasance mazinaciya Koda tatuba daga baya dole sai y'ay'anta sunyi Koda Bada son ransu bane tofa sai Wani ya b'atasu, haka Kuma idan Namiji yakasance mazinaci kafin aurensa dama bayan Auransa to wllh indai zai haihu kai Koda namiji zai Haifa Bada Macce to wllh saisun Gade halinsa dole suyi Koda Bada sanransu ba sai Anyi dasu, idan kuwa Baka Haifa to za'ayiwa Matarka, idan ba Matar ba Mahaifiyarka koma dai Wani d'an uwanka nakusa dakai mafi kusanci wllh dole saiyayi Domin duk Abunda kashuka shizaka girba, *AKAN AIKINKA* kazab'e sharholiyarka, kazab'e banzatarda ni Matarka Dama mutuncina yanzu gashinan *AKAN AIKINKA* Wani ya b'atawa y'arka tarbiya, Kuma Bari kaji ingaya Maka daga k'arshe nikaina saika sakeni dole karabu Dani bazan iya cigaba da zama dakaiba kaidai ita kujecan ku k'arata saika fad'awa duniya cewar *AKAN AIKINKA* y'arka talalace Kuma karabu da Matarka nidai bazan iya gayawa duniya cewar *AKAN AIKIN MIJINA* y'ata tayi cikin shege ba, *AKAN AIKIN MIJINA* Tarbiyar da nayiwa y'ata yalalace zan iya fad'in cewar *AKAN AIKIN MIJINA* narabu dashi dole kasakeni Dr Faisal *AKAN AIKINKA*," tana gama maganar tature Khairat daga jikinta tabar d'akin hawaye masu zafi suna silalomata, 



Shikuwa jirine yaji yana d'aukarsa dafe Kansa yayi da saifin Zuciyarsa Dake tsananta bugawa take yafad'i gurin,



Kansa Khairat Tayo tana ihun Kiran Ummanta tareda jijjigashi tana fad'in"Dan Allah Abba kuyi hak'uri kuyafemun wallahi bazan k'araba, Umma Dan Allah kiyi hak'uri kizo," khaleepha ne k'anenta yafara shigowa d'akin cikin tashin hankali Yace"kashe mana Mahaifin kikayi ko wato har rashin tarbiyar takaiga k'ok'arin Raba iyayenmu Kuma kike k'ok'arin hallaka Abbanmu, to wllh ke Zaki fara halaka kafinsu, belts d'insa yazare yasoma jibgarta kota Ina yana shurinta da k'afa har yasamu damar shurin maranta kuma takata da k'arfi, Ihun Azaba tasaki da k'arfin gaske Wanda yasaka Yasmin shigowa babu shiri jinin taga yana bin k'afafuwanta kasa magana tayi kawai illa fita waje datayi takira driver d'insu yataimaka Musu suka fita dasu zuwa Asibiti, dukansu Ashiga dasu Akasoma basu taimako.........




Daddy dakansa yasoma Kiran wayar Abba ai Kuwa ya d'auka sukagaisa"yace gamu munsauka A hotel Muna son zuwa inda kuke muga maijiki,"




"Oh to Masha Allah tana Asibitin ai kasan Nan bakar Nigeria bane mukuwa mundawo inda muka sauka, sai zuwa gobe zamu koma Asibitin"





"Masha Allah to jikin da sauk'i daiko,"?




"Eh Alhamdulillah"




"Idan badamuwa Dan Allah kozaka bamu damar zuwa inda kuka sauka,"?





"Ok zantura maka address D'in hotel"

Gdy yamasa gamida sallama suka Aje wayar






"Kaga bazama zamuyi ba kawai mujecan yanzu musamesu"



Mik'ewa sukayi suka nufe hotel D'in, basusha Wahala ba sukagano hotel D'in




Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa, Sosai su Abba da hajiya dama shi kansa Dr Muhayseem suka Bada hak'uri



Abba Yace"to komai yawuce Allah yasa mudace, saidai bazan yake Hukunci kan Rayuwarta ba A wannan karon kuyi hak'uri dai idan tasamu sauk'i saimuji tabakinta,"





"Bakomai Alhaji duk dahakan aimune da godiya,"



Shidai hankalinsa yakasa Kwanciya har sukadawo Nigeria Domin fir Auntie kubra tahana yaganta ko iyayen nasa Basu samu ganinta ba gashi baisamu ganin Dr Sabeer ba dole ya hak'ura suka dawo,




Sati d'aya tayi tawarke sosai sukadawo Nigeria kulawa sosai take samun gurin iyayenta da Auntie kubra saidai har lokacin aunty kubra tak'i sauka, saidaga bayane ma su Hajiya sukasan sundawo Nigerian Hakan yasa suka shirin tafiya dukansu, 


Sunsha mamaki ganinta da d'anta kyakykyawa kamar Antsaga kara da Dr Muhayseem, Anan ne suka samu labarin da Yara 2 ne sai gudan yamutu tun ciki yabar d'aya, hajiya taji dad'i sosai naganin jikanta yaron Dr Muhayseem sosai sukayi Murna, 





Yau kusan wata d'aya Kenan baisake zuwa Aikinsa hatta wayoyinsa duka yakashesu ya kulle kansa A d'aki shikad'ai ko Abincin kirki baici yayi wata muguwar rama yayi Bak'i yataran k'asumba kamar Wani d'an gidan yari haka yadawo bawani gayu bawani bawa Aiki Mahimmanci kullum yana cikin K'unci sallah kawai ketashinsa daga kwance sai Zaune ko sallan cikin d'akin yake banda cake da lemu babu Abunda yakeci,



Hatta ma'aikatan gidan sunga banbanci Yanzu harma tausayinsa sukeji,




Cikin Farinciki hajiya tazo gidan gaidata baba Audu ta Ansa cikin sakewa tace"yana gidan kuwa,? Koyatafi Aikin,"?




"A'a hajiya yana ciki, gwandama da Allah yakawoki dan wllh zamansa gidan dakwai cutarwa sallah yanzu yadaina fitowa mukanmu Dake cikin gidan wallahi yau sati uku kenan bamu sakashi a idanmu ba, magiya da rok'o kan yafito bawanda bamuyi ba Amma Wllh Hajiya baisauraremu kullum saina rok'eshi Koda bazai fito ba ya k'arb'e Abinci yaci Amma fir yak'i Yanzu haka zamanda nake jiran sale nake yadawo yacan gida yasameku ya fad'amuku halinda Ake ciki,"





"Subhanallahi bari nashiga nagansa"


K'ofar parlour Bud'e take shiga tayi duk yayi k'ura saboda bamai gyara kuma babu Wanda yake Zaune cikinsa, bedroom D'insa tanufa saidai babu Alamarsa ciki Hakanyasa tagane yana d'akin Muhseenarh dai, Murd'a handle D'in k'ofar tayi Amma rufe d'akin yake nocking tayi Amma Shuru, Hakan yasa tabud'e murya tace"Haba son kashe Kanka kashiryayi? Wannan matakin daka d'auka Atunaninka shine zaibaka solutions? Kakashe duka wayoyinka komai naka yatsa cak duka saboda me? Kaga kabud'emun k'ofar inasonyin magana dakai,"





Zaune kawai yake kan sallayan da yayi sallan Assuba haryanzu baitashi ba gurin sanye yake cikin jallabiyansa faraqal idansa sunyi wanija sosai d'aga kansa kawai yayi yana jiyo maganar hajiya Amma yakasa tashi ya Bud'e k'ofar, shifa yanzu Maganar kowa baya buk'ata kawai Abashi yagirbe Abunda yashuka ai *AKAN AIKIN* sane yajamasa matsalar to barshi *AKAN AIKIN* Kuma ya hukunta kansa, gashi *AKAN AIKINSA* wata 1 d'aya Kenan baida Labarin matarsa kota Mutu kotana Raye baisani ba, *AKAN AIKINSA* Yakasa samun yara shikan *AIKINSA* Bai k'are shi dakomai ba face nadama dama Bak'in ciki, 


Umma tace"Kinganmun ja'iri waifa yayi Shuru, ai Kuwa zakayi bayani duk randa kazomin gida,"




Dariya sukayi dukansu,



Ba'ad'auke Wani lokacin ba Aka sallameshi,


Zama na Musamman Akayi tadeda iyayensu nanne take Bada Labarin dakwai Aljanin Agidan bazata iya komawa cikinsa ba saidai yanemamata wani,



Tun Anan Daddy yabasu Wani gidan kansu komacan waccan kuwa za'ayi masa karatu


Hakan kuwa takasance saiga Aljanin yabayyana bayan Mlm yayi karatunsa Nan yake fad'in shi turosa Akayi Adaina k'onasa,




Mlm sani yace"waya turoka to,"





*Ubangidana shine yaturoni Shima Aiki Akabasa sunanta Zeeza itace Silan zuwana nan, Kuma nasamu damar bata wahala ne dama shiga gidan Saboda sakacinda tafara Kuma bamusamu damar samun sakacin nataba Saida ta shagala da Damuwa *AKAN AIKIN MIJINTA* tanan muka samu damar Aiwatarda komai"




Cikin mamaki Dr Muhayseem yace"Zeeza"?



Mlm yace"kasanta ne,"? 



"K'warai kuwa Mlm nasanta"




"To daga baya mayi magana Kanta,"




"Yanzu Kai inason karabu da bayin Allah Nan duka kafita Rayuwarsu har Abada,"




"Ni bazan iya sab'awa Ubangidana ba, Domin Akwai Amana tsakaninmu"




"To ai shikenan kaida Ubangidan naka Kuwa duka zaku mutu Kuma Allah zai Muku Hisabi kafin kaje katarda naka Hisabin kafin kaje Yanzu zan k'onaka,"


Ayoyin Qur'ani yashiga karantamasa 



Ihu yafara zanfita zanbar gidan zanbar Rayuwarsu, kadakata zantafi,




Dakatawa Mlm Yayi kamar hayak'i haka yatashi sama yabi tacikin Celine yatafi




"Masha Allah yanzu dai babu Wani ragowar Wani iska tareda ku saidai Kaine zaka k'ara dagewa gurin bawa Matar kulawa hankalinta kwanta tanan zatasamu damar Maida hankali kan ibadarta itama, kudaina d'aukar Imaninku kacokam Kuna d'aurawa *AKAN AIKINKU* Wani wllh saboda AIKINSA baidamu da ibadaba Wani sharholiyar yasake bako tuna mutuwa, Musamman wannan zamanin saikaga Mutane masu Aikin Asibiti dama Malaman boko saikasamesu dayawan ma'amala da matan banza Wanda sune kawai suka d'aurawa kansu wannan bak'ar Agida bazanso Jin ko wacce garekaba Amma Dai kagani Kaga Abunda yafaru yabzu saika kiyaye gaba kamaida hankali Kuma kaji tsoron Allah *AKAN AIKINKA* Domin shikanshi *AIKIN* naka Abun tanbaya ne gareka gobe k'iyama saboda haka sai A k'ara kula Allah yakaremu," 




"In sha Allah Mlm zamu kula mungode sosai"






"Kai Ina taya Hakan zata faru haba boka bakamun Alk'awarin zasu rabu ba taya yanzu Kuma zakace Aljanin yadawo amma...." 





"Ke rufemin Baki Anan Ina Miki maganar Ank'onamin Aljanina kinamun zancen banza shasha kibar gurin Nan kafin Raina yab'aci Kuma keda Aure har Abada Domin wannan Aljanin damuka tura yafusata Yanzu haka Ina biye Dake dashi Zaki Rayu,"




Mik'ewa tayi cikin firgici tabar gurin bokar tana waige waige harta kawo bakin tatin Sam bata cikin hayyacinta batareda taduba ba taje tsallake titin take wata k'atuwar mota tabi takanta Nan take mutuwarta taziyarceta,,






Yanzu basuda damuwar komai sai Farinciki da Walwala gamida k'aunar juna Saida tanuna fushinta da b'acin ranta kafin tasamu Dr Muhayseem yakoma kan Aikinsa,..



BAYAN SHEKARA UKU





A yanzu yaransu Dr Muhayseem 5 Maza 2 mata 3, inda su Yasmin kuwa yaransu 6 su khaleepha da Khairat kuwa Anyi Aure,



Zaune suke iyayen suna fira suna dariya cikin raha,



Yasmin tace"Yanzu dai *AKAN AIKIN MIJINA* Ina Alfahari dashi, tafad'a tana Kashe masa ido d'aya,




Muhseenarh tace"to nidai yanzu *AKAN AIKIN MIJINA* ai saidai sanbarka da k'arin soyayya Yarda nake samun kulawa kuwa ai ko jinjiri Albarka, sab'anin da danakejin *AKAN AIKIN MIJINA* gwanda Rabuwa to yanzu *AKAN AIKIN MIJINA* Saidai mutuwa nidashi,"





"Nikaina Saida na k'ara Banda hak'uri Kuma kullum ina cikin godiya ga Allah daya bani ikon gyara halina *AKAN AIKINA* Kuma nasamu damar faranta ran matana *AKAN AIKINA* Dr Muhayseem ya fad'a yana rungumarta





"Nikaina danafi kowa b'arna *AKAN AIKINA* yanzu saidai nace Alhamdulillah Kuma hak'ik'a samun Macce Mai ilimin Addini wllh baiwane Kuma dace Allah yak'ara tsaremu da Imaninmu dama *AYUKANMU*,"




Da Ameen suka Ansa dukansu cikin Farinciki da nishad'i,............. 





TAMMAT BI HAMDULLAH 



ANAN KAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN NAWA, ALLAH KABANI LADAN ABUNDA NAYI MAIKYAU ACIKI INDA MARA KYAU KUMA ALLAH YAK'ARA KAREMU DUKANMU KUMA ALLAH YABAMU IKON GYARA RAYUWARMU DAMA GOBENMU,.. 



KUMA INASON KUSANI YAWAN LITTAFI BASHINE KYAWONSABA , ZAYYANA FITSARA KO BATSA BASHINE KYAWON LITTAFI BA, ABU MAFI KYAU SHINE KATSAYA CIKIN NATSUWA KAYI LABARI WANDA ZAIBADA MA'ANA DA WA'AZANTARWA DAMA FAD'AKARWA GAMIDA ILIMANTARWA......ALLAH YASA MUDACE 🤲 SAIMUN SAKE HAD'EWA CIKIN LITTAFINA NAGABA, TAKU HAR KO YAUSHE ✍️ MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR QUEEN OF WRITER'S HAUSA NOVELS 📚📖📚 AND DESIGN GRAPHICS.



DAGA QARSHE KUMA INA FARAIN CIKIN SANAR DAKU CEWA: INA TURA KOWANE SERIES FILM ACIKIN SAUQI AKAN LOKACI, SANNAN KUMA AKAN FARASHI MAI RAHUSA 🙌 

DUK WANDA SUKE SON A TURA MUSU ZASU IYA YIMIN MGN T TELEGRAM KO WHATSAPP A WNN NUMBER 👇 

09032116442. 

INAI MK FTN ALKHAIRI 🙌 NGD 🙏 

Post a Comment

247 Yawa Trends Reserves our Rights on Any Comments by our Viewers, As they have nothing in connection to 247 Yawa Trends

Previous Post Next Post