🌸 SAAKK – Episode 132 (Part A) 🌸
Anokhi ta juya a hankali wajen Shaurya tana tambayarsa:
“Ya akai ka zo nan da wuri haka?”
“Yaya jikinka?”
Sai ya rufe mata baki da yatsansa, sannan ya ja ta da sauri zuwa wani bangare daga wajen.
Anokhi ta kara tambayarsa cikin damuwa:
“Yaya kake?”
“Me likitoci suka ce?”
Shaurya ya sake rufe mata baki da yatsansa sannan ya ce:
“Ina bukatarki fiye da yadda nake bukatar likita.”
“Ina bukatar ganinki, Anokhi.”
“Akwai abubuwan da nake son fada miki… ki saurare ni.”
“Da farko dai, ina son sanin menene abin da kike son fada min? Wani abu ne kullum yake shiga tsakaninmu a tsakiyar maganar.”
Shaurya cikin yanayi ban tausayi ya ce:
“Ina son ji, Anokhi. Ba zan iya jira ba… ba zan iya sake jira ba kuma.”
“Kin san cewa ko lokacin da ban da lafiya, da kuma lokacin da aka yi garkuwa da ni, ina ci gaba da yin tunani akanki.”
“Don Allah, kada ki sa ni jira, Anokhi… kada ki yi min haka.”
Yadda yake maganar sai ka tausaya masa. Anokhi kuwa ta kasa dauke idonta daga kansa cike da tausayi da soyayya 💞
Kafin ya karasa rufe bakinsa, ta fada abin da yake son ji:
“Ina sonka, PS.” ❤️
Sai shi ma ya amsa cikin wani irin yanayi mai ratsa zuciya:
“Ina sonki, Ms Bhalla.”
(Ya kira ta da tsohon sunanta, wanda kusan ta manta da shi.)
Nan suka fara maimaita kalmar “Ina sonka / Ina sonki” cikin wani irin yanayi mai zafi da soyayya 💕
hugging dinta yai d qarfi, ita m t riqe Shi Sosai cike d farin ciki , ydd suke je kmr dny t tsaya chak a wnn yanayin, SE kuma y jata wani bangaren suka har ma suka yi rawa cikin farin ciki. Har suka fadi a kasa saboda nishadi 😍
Dariya da farin ciki ba za su misaltu ba a fuskokinsu.
💫 Bayan Hakan…
Anokhi ta ce tana murmushi:
“Duniya baki daya tana zagayawa.”
Shaurya ya ce:
“Ni ma haka.”
Sai ya dago daga kwanciyarsa yana kallon fuskarta ya ce:
“Mun yi yawo, sannan muka sake haduwa da juna.”
“Kin san wani abu kuma?”
“Kin sa ni jira tsawon lokaci… amma a karshe na ji abin da nake son ji.”
“Ina jiran wannan tun ranar birthday party dinki.”
Sai ya shafa fuskarta ya ce:
“Amma a yau kin fada min.”
Ya rike hannunta ya sumbaci hannun yana cewa:
“Ni ne mutumin da ya fi kowa sa’a a duk fadin duniya.” ✨
😢 Sauyin Yanayi
Tin lkcn d ambaci birthday party dinta, sai ta tuna da abin da ya faru a lokacin… musamman sanarwar da Ms Devi ta yi game da aurensa da Shagun.
Sai tunaninta ya sauya… ta ja hannunta daga nasa, ta mike ta juya gefe, idanunta cike da hawaye.
Shaurya ya bi ta da sauri yana tambaya:
“Lafiya?”
“Me ya faru?”
“Me ya kawo wannan sauyin lokaci guda haka?”
Seya matso kusa d ita Ya kwanto da kansa a jikinta, ya rungume ta yana kokarin kwantar mata da hankali.
Anan Part A ya kare.
Za mu hadu a Part B Insha Allah.
👉 Wadanda suke son Part B ya iso gare su, su yi sharing Part A a groups 20 sannan su turo min screenshot a private.
📢 NOTE:
Ina tura kowane irin series cikin sauki, akan lokaci, kuma akan farashi mai rahusa 🙌
Masu bukata su tuntube ni ta Telegram ko WhatsApp a wannan number 👇
📱 09032116442

Post a Comment
247 Yawa Trends Reserves our Rights on Any Comments by our Viewers, As they have nothing in connection to 247 Yawa Trends