Za ka iya zama billionaire a cikin ’yan sakanni a Ethereum Blockchain
Menene Flash Loan?
Kafin mu shiga bayanin Flash Loan, yana da kyau mu fara da fahimtar traditional loan wanda bankuna da sauran institution na kuÉ—i ke bayarwa.
Loan (bashi) kuÉ—i ne da banki ko wata institution na kuÉ—i ke bayarwa ga mutum ko kamfani, da sharadin:
za a dawo da kuÉ—in a wani lokaci,
tare da ƙarin kuɗi da ake kira da interest.
Misali:
Idan banki ya baka bashin ₦100,000 da 10% interest, hakan yana nufin cewa:
za ka dawo da ₦110,000 (₦100,000 + ₦10,000).
Matsalar Traditional Loan
Babbar matsalar wannan tsarin ita ce:
mutum zai iya karɓar bashinka ya ƙi mayar maka a lokacin da aka tsara.
Saboda haka, bankuna suke neman abun da ake kira da collateral.
Misali:
Idan banki zai baka bashin ₦10,000,000, zai iya karÉ“ar takardar gidanka ko wata dukiya mai daraja.
Idan ka kasa biyan bashin da interest din yanda aka tsara, banki zai sayar da wannan dukiyar taka ya cire kuÉ—insa.
Yadda Blockchain da Smart Contracts suka magance wannan matsalar
A cikin Ethereum Virtual Machine (EVM) da Smart Contracts:
idan kana son karɓar bashi, dole ne kai lock na wani asset mai darajar da ta kai ko ta fi na bashin.
Idan ka kasa biyan bashin:
tsarin zai yi liquidating naka automatically.
Menene Flash Loan?
Flash Loan wani irin rance ne a bangaren Decentralized Finance (DeFi) na Ethereum, inda:
za ka iya karɓar kuɗi mai yawa sosai,
ba tare da collateral ba,
amma da sharaÉ—i guda É—aya mai tsauri:
dole ne ka mayar da rancen gaba É—aya a cikin transaction guda É—aya.
Idan baka mayar ba:
duk transaction ɗin zaiyi failing (revert) kamar ba a taɓa yin komai ba.
Ta yaya Flash Loan yake aiki?
A Ethereum, duk abin da ke faruwa a cikin transaction guda É—aya yana bin ka’idar atomicity:
ko dai komai ya yi success, ko kuma komai ya failing ya rushe.
Steps din sune kamar haka:
Ka nemi Flash Loan (misali 1,000,000 USDC)
Ka yi wani aiki da kuÉ—in, kamar:
arbitrage
liquidation
swap
Ka biya rancen tare da biyan kuÉ—in fee(interest)
Transaction ya kammala
Idan ba ka biya ba:
Ethereum zai soke komai yayi reverting.
Me yasa Flash Loan baya bukatar Collateral?
Saboda tsarin Ethereum yana da tabbacin cewa:
idan ba ka biya ba, ba za a bar transaction É—in ya kammala ba.
Saboda haka, mai bayar da rance (lender) ba ya shiga haÉ—ari.
Misali Mai Sauƙi
Ka É—auka:
farashin ETH a DEX A = $1,900
farashin ETH a DEX B = $1,950
Abin da zaka yi da Flash Loan:
Ka karɓi Flash Loan na $1,000,000
Ka sayi ETH a DEX A
Ka sayar da ETH a DEX B
Ka biya Flash Loan da fee
Abin da ya rage ribarka ce
Duk wannan yana faruwa ne a cikin transaction guda É—aya.
Ina ake amfani da Flash Loan?
Ana amfani da Flash Loan wajen:
arbitrage
liquidation a lending protocols
debt refinancing
collateral swap
advanced DeFi strategies
Protocols da ke bayar da Flash Loan:
Aave
Balancer
Uniswap (flash swap)
Hadarin Flash Loan
Amfani da flash Loan kansa ba hatsari bane, amma ana iya amfani da shi wajen:
price manipulation
oracle attacks
exploiting vulnerable smart contracts
Saboda haka yawancin manyan hare-haren DeFi suna amfani da Flash Loan.
Note: tsarin loans da ake biyan 'kari fiye da abun da aka ara riba ne, riba kuma haramun ne da nassin Qur'ani.
Zaka iya shiga course namu na Solidity Blockchain Development a Flowdiary.ai

Post a Comment
247 Yawa Trends Reserves our Rights on Any Comments by our Viewers, As they have nothing in connection to 247 Yawa Trends